Tinubu Zai Nada Jakadu bayan DSS Ta Mika Sunayen Mutanen da Ta Tantance
- Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa yanzu haka hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kammala aiki a kan sunayen jakadun kasar nan
- Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye dukkanin jakadun kasar nan da ke aiki a kasashen duniya daban-daban
- Majiya daga fadar shugaban ta bayyana cewa ana jiran Tinubu ya kammala duba jerin sunayen da sanya ranar aika wa ga majalisa domin tantancewa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi sabon jerin sunayen waɗanda za a naɗa jakadun Najeriya a kasashe daban-daban.
Majiyoyi daga fadar Shugaban kasa sun bayyana cewa yanzu abin da ya rage shi ne a sanya ranar da Tinubu zai aika jerin sunayen zuwa majalisar dattawa.

Source: Facebook
A labarin da ya kebanta ga jaridar Punch, an ruwaito cewa tuni aka kammala duk binciken tsaro da bayanan sirri wanda hukumar DSS ta yi.
Bola Tinubu ya karbi rahoton DSS
Rahoton ya kara da cewa yanzu haka ana jiran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya amince da jarin sunayen da aka aika masa.
Wata majiyar gwamnati ta ce:
"An gama aiki a kan jerin sunayen, Yanzu yana kan teburin shugaban ƙasa. Shi ne zai yanke ranar da za a tura shi majalisa.”
Majiyar ta ce shugaban ƙasa ba zai fitar da duk sunayen jakadu baki ɗaya ba saboda nauyin kuɗin da ake bukata wajen tura su ƙasashe daban-daban.
Za a fara da manyan ƙasashen abokan hulɗa kamar Amurka, Birtaniya, ƙasashen Tarayyar Turai, China, India da muhimman ƙasashen ECOWAS.
Tinubu zai tura jakadu kasashen duniya
Rahoton ya kara da cewa Najeriya na da alaƙa ta kasuwanci, tsaro da siyasa da waɗannan ƙasashe da za a fara aika jakadu, inda Turai ta zama babbar abokiyar hulda
China da India kuma na taka muhimmiyar rawa a ayyukan makamashi, tituna, tashoshi da layukan dogo.

Source: Facebook
A Afrika, biranen Accra, Niamey da Kwatano na daga cikin muhimman wuraren da ake turawa jakadu saboda rawar da Najeriya ke takawa a yankin.
Wannan mataki na zuwa ne bayan shekaru biyu da Tinubu ya janye dukkannin jakadu daga ofisoshin jakadancin Najeriya 109 a 2023 domin sake fasalin tsarin diflomasiyya.
Tun daga wancan lokaci, manyan ofisoshin jakadanci sun kasance a hannun ‘chargés d’affaires’, wadanda ba su da cikakken hurumin wakiltar ƙasa a manyan tattaunawa.
Shugaba Bola Tinubu zai bar Najeriya
A wani labari, kun ji cewa Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai tafi Johannesburg, don halartar taron G20 da za a yi daga ranar 22 zuwa 23 ga Nuwamba, 2025.
Daga nan, bayan taron G20, Tinubu zai kara tafiya zuwa Luanda, Angola, domin halartar taron haɗin gwiwar Majalisar Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da Tarayyar Turai (EU).
A cewar fadar shugaban ƙasa, kasancewar wannan taro na G20 shi ne na farko da za a gudanar a nahiyar Afrika, zai bayar da dama wajen nuna wa duniya muhimmancin kasashen yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

