Mayakan ISWAP Sun Sake kai Hari kan Sojoji a Borno, an Rasa Rayuka

Mayakan ISWAP Sun Sake kai Hari kan Sojoji a Borno, an Rasa Rayuka

  • Garin Mayenti a Bama ya sake shiga tashin hankali bayan 'yan ta'addan ISWAP sun kai hari, inda 'yan sa-kai huɗu suka mutu
  • Rundunar Operation Hadin Kai ta yi artabu da mayakan a harin ya zo bayan ISWAP ta saki bidiyon kashe Birgediya Janar M. Uba
  • Harin ya kara tayar da hankalin jama’a kan yawan matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Borno – Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da sabon hari da kungiyar ISWAP ta kai kan wasu soji da ke Mayenti, cikin Karamar Hukumar Bama.

An bayyana cewa harin ya jawo asarar rayuka a bangaren 'yan sa-kai da kuma shafar wasu dakarun sojojin Najeriya.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Premium Times ta wallafa cewa farmakin ya auku ne jim kadan bayan sakin bidiyon kashe Birgediya Janar M. Uba da kungiyar ISWAP ta wallafa.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin ya sake tunzura fargaba a yankin, musamman ganin cewa Mayenti na daf da Dara Jamal, wurin da aka kashe mutane sama da 60 a baya.

Yadda ISWAP ta kai sabon hari Borno

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa harin ya faru a daren Litinin, inda mayakan ISWAP suka kutsa cikin garin cikin daruruwan babura.

Dakarun soji sun yi artabu da su na tsawon lokaci, lamarin da ya haifar da kashe da dama daga cikin mayakan.

Rahoton Blue Print ya ce masu taimakawa sojoji wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin, wato CJTF, guda huɗu sun rasu yayin fafatawar.

A yayin da mayakan ISWAP suka ja da baya, sun kona motocin wasu masu aiki guda biyu sannan suka kashe ma’aikata huɗu da suka tarar suna aiki a yankin.

Wannan ya ƙara tsoro ga mazauna yankin, musamman ganin irin yadda hare-hare ke ƙaruwa kwanakin nan.

An kai harin bayan kashe Birgediya Janar

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka mamaye GGCSS Maga da harbi kafin sace dalibai mata a Kebbi

Harin ya zo ne sa'o'i bayan mayakan ISWAP sun saki bidiyon kisan Birgediya Janar Uba, wanda ya bata tun bayan harin da ya tsira daga cikinsa a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce ya rasa damar tuntuɓar rundunarsa yayin da yake jiran agajin sojoji, sai 'yan ta’adda suka same shi suka kashe.

Shugaban rundunar tsaron Najeriya
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Oluyede. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Wannan lamari ya tada hankulan 'yan Najeriya, inda jama’a da dama suka bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa na murkushe ta’addanci a Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasa.

Managar Gwamnan Borno kan rashin tsaro

A yayin da ake ci gaba da kira ga daukar mataki, gwamnan Babagana Zulum ya nemi gwamnatin tarayya ta samar da karin jiragen sintiri da kuma fasahohin zamani don taimakawa sojoji.

A cewarsa, dole ne a yi amfani da dabaru na zamani wajen shawo kan 'yan ta’adda da suka addabi mutanen Borno da kewaye.

An kai hari kan makiyaya a jihar Benue

A wani labarin, kun ji cewa wasu makiyaya sun koka da yadda aka kai musu hari a wasu yankunan jihar Benue.

Kara karanta wannan

Shugaban sojoji ya dura Kebbi, ya ba dakaru umarni kan daliban da aka sace

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shanu kusan 300 a yankunan da aka kai harin a kananan hukumomi biyu na jihar.

Wasu makiyayan da aka yi wa barna sun bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa domin magance matsalar da suke fuskanta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng