Kawu Sumaila: An Daura Auren Sanatan Kano da Hindatu, Jami'ar Sojojin Najeriya
- Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya angwance da amaryarsa Hindatu Adda’u Isah, jami’ar sojojin saman Najeriya
- An daura auren ne a fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umar, lamarin da ya jawo cece-kuce saboda ya zo a ba-za-ta
- Manyan mutanen da aka hango sun halarci daurin auren Kawu Sumaila sun hada da A.A. Rano da Kabiru Alhassan Rurum
Kano - Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya angwance da Hindatu Adda’u Isah a Kano.
Sanata Kawu Sumaila dai shi ne sanatan da ke wakilatar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, kuma ya auri Hindatu, wacce jami'ar sojojin saman Najeriya ce.

Source: Facebook
An daura auren Sanata Kawu Sumaila
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an daura auren ne a ranar Litinin, a fadar Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Auren, wanda aka daura shi ba tare da an yi shela a kafafen sada zumunta ba, ya jawo hankulan mutane, musamman bayan ganin hotunan sanatan da amaryarsa.
Daya daga cikin hadiman Kawu Sumaila, Muttaqa Babire, ya tabbatar da daura auren sanatan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
Muttaqa ya wallafa hotunan Sanata Kawu Sumaila da amaryarsa, Hindatu Adda’u Isah, wacce take sanye da kakin sojoji.
Hakazalika, wani hadiminsa, Ahmad Tijjani Salisu Kirsu, shi ma ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Alhamdulillah, an daura auren Sanata S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D a garin rano a yau 17-11-025, Allah ya sanya albarka, amin.
"Ubangiji Allah ya ba da zaman lafiya tare da zuri'a dayyaba, Amin ya Rabbil Alamin."
A.A Rano sun wakilci Sanata Kawu Sumaila
Babu wata sanarwa da aka yi game da wannan auren, kawai dai an ga hotunan lokacin da ake daura auren, inda aka ga wasu manyan mutane a fadar sarkin.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa, Alhaji Auwalu Abdullahi, wanda aka fi sani da A.A. Rano da kuma Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar Rano, Kibiya da Bunkure a Kano ne suka wakilci Sanata Sumaila a wajen daurin auren.
Rahoton ya kuma nuna cewa an gudanar da wannan auren ne bisa sunnar Annabi, yayin da ake ci gaba da tsumayin fitowar karin bayanai.
Sanata Kawu Sumaila dai shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa na albarkatun man fetur (na ruwa), kuma a baya-bayan nan ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

Source: Twitter
'Yan Najeriya sun yi martani kan auren Sumaila
Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin ra'ayoyin jama'a game da wannan aure na Sanata Kawu Sumaila.
Misbahu Ibrahim:
"Allah ya sa albarka ya kawo zuri'a mai albarka, wallahi ka yi dacen mata mai hankali, na ba ta horo, na san halinta da yadda take, yallabai Allah ya sa alkairi amin."
Babaji Safiyanu:
"Allah ba su zaman lafiya. Amma dai dolen ta tana kasan shi duk da sojan sama ce. Ehe!"
Sani Muhammad:
"Masha Allahu, Allah ya sanya albarka a cikin rayuwar su."
Muhammad Rajab:
"Shi Sanata ne kuma mai kudi, za ta yi masa biyayya. Amma talaka ya kuskura ya kai kansa, hmmm, sai dai muce Allah ya kyauta amin."
Umar A Usman Cham"
"Madallah ango. Nasihar mu ga amarya ita ce, ki sani ba a sa sanata tsallen kwado ko da ya yi laifi."
Hassan Abkr:
"Gaskiya ba karamin birgeni yayi ba."
Dalilin Kawu Sumaila na komawa jam'iyyar APC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sanata Kawu Sumaila ya bayyana cewa ficewarsa daga jam’iyyar NNPP na da alaka ta kai tsaye da mutanen Kano ta Kudu.
A cewarsa, ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne saboda yana son ci gaba da kawo wa mazabarsa mafita da ci gaba da ba zai samu a NNPP ba.
Dan majalisar dattawan ya ce ko da yake ya fice daga jam’iyyar da ke mulki a Kano, hakan ba zai kawo wata matsala a dangantakarsa da gwamnatin jihar ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


