Naira Tiriliyan 1.4 Sun Yi Kafa a CBN, An Taso Gwamnan Babban Banki Ya Yi Bayani

Naira Tiriliyan 1.4 Sun Yi Kafa a CBN, An Taso Gwamnan Babban Banki Ya Yi Bayani

  • SERAP mai kare hakkin jama’a da inganta shugabanci ta fusata bayan wani rahoto ya ce N3trn sun bace daga asusun babban bankin Najeriya
  • Kungiyar ta bai wa gwamnan CBN, Olayemi Cardoso kwanaki bakwai ya yi bayanin yadda kudin suka yi layar zana daga asusun babban bankin
  • SERAP ta nemi a tona sunayen masu hannu a cikin zargin ɓarnar tare da miƙa su ga ICPC da EFCC domin bincike da gurfana da su a kotu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar kare hakkin jama’a da inganta shugabanci, SERAP, ta mika bukata ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso.

Kungiyar na neman cikakken bayani kan abin da ta kira ɓacewa ko karkatar da N3trn na kuɗin jama’a kamar yadda ya bayyana a rahoton shekara-shekara na ofishin dake sa ido kan al'amuran kuɗi na 2022.

Kara karanta wannan

An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP

SERAP ta taso gwamnan babban bankin Najeriya a gaba
Olayemi Cardoso, gwamnan CBN Hoto: Central Bank of Nigeria
Source: UGC

Nigerian Tribune ta wallafa cewa wannan rahoto, wanda aka wallafa a ranar 9 ga Satumba 2025, ya bayyana yadda aka saba wa dokokin kuɗi da tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SERAP ta sako gwamnan CBN a gaba

Jaridar Leadership ta wallafa cewa a cikin wasikar da aka rubuta a ranar 15 ga Nuwamba, wadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya zargi CBN da karya doka.

Kungiyar ta ce abubuwan da ofishin dake sa ido kan al'amuran kuɗi na 2022 ya gano na nuni da take doka, rashin gaskiya da tauye amanar jama’a.

SERAP ta ce za ta kai CBN kotu kan batan kudi
Hoton gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso Hoto: Central Bank of Nigeria
Source: Getty Images

SERAP ta ce irin waɗannan matsaloli suna rage martabar CBN a idon al’umma kuma suna raunana ikon sa na cika nauyin da doka ta dora masa.

Ta bayyana wasu muhimman abubuwan da rahoton ya bayyana, daga ciki har da rashin tura sama da N1.4trn na ribar aiki zuwa Asusun Tarayyar Ƙasa (CRF) kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Mata 6 da suka sha ƙasa a zaben gwamna a zaɓukan Najeriya

Rahoton ya kuma nuna cewa ba a san sunayen mutanen da suka ci gajiya N629bn a karkashin tallafin shinkafa da gwamnatin ta bayar ba.

Kudi sun bace a asusun CBN

SERAP ta ce bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa har yanzu ba a dawo da lamuni N784bn da aka bai wa jama'a domin su cicciba kawunansu ba.

Wani ɓangare mai muhimmanci na rahoton ya nuna cewa CBN ta kasa tura fiye da N1,445,593,400,000.00 da ya rataya gare ta.

Haka nan SERAP ta yi nuni da cewa CBN ta kashe sama da N1.7bn wajen sayen motocin aikin Jami’an Shige da Fice (NIS), abin ta ce ba shi da alaka da manufar CBN.

CBN ya magantu kan darajar Naira

A baya, mun wallafa cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce duk da tsananin faɗuwar darajar Naira a kasuwannin cikin gida da na waje, har yanzu akwai manyan damarmaki ga kasar nan.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana haka yayin wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, 16 ga Oktoba 2024, inda ya ce ya kamata a ribaci wadannan damarmaki.

Kara karanta wannan

A.M Yerima: Tsohon jigon APC, Frank ya shawarci Tinubu ya ja kunnen Wike

A cewar Cardoso, faɗuwar darajar Naira ba wai kawai matsala ba ce ga tattalin arzikin ƙasa, amma dama ce da za ta iya taimaka wa Najeriya ta bunƙasa fitar da kayanta zuwa waje.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng