Kebbi: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Kwana, Sun Sace Dalibai Mata Masu Yawa

Kebbi: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Kwana, Sun Sace Dalibai Mata Masu Yawa

  • 'Yan bindiga dauke da ke dauke da miyagun makamai sun kashe mataimakin shugaban makarantar mata ta GGCSS, Maga
  • An ce 'yan ta'addan sun kai hari makarantar kwanan ne a daren Lahadi, inda suka sace dalibai mata masu tarin yawa
  • Wata mata da lamarin ya faru a kusa da su, ta bayyana yadda maharan suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - An shiga tsananin tashin hankali a masarautar Zuru da ke jihar Kebbi biyo bayanin wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai cikin dare.

An rahoto cewa, 'yan bindiga masu tarin yawa, dauke da miyagun makamai sun farmaki makarantar kwana ta mata (GGCSS) Maga.

'Yan bindiga sun farmaki makarantar kwana ta mata, su sace dalibai masu yawa.
Taswirar jihar Kebbi da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun sace dalibai mata a Kebbi

Makarantar mata ta GGCSS Maga dai ta na a cikin karanar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

Kara karanta wannan

An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da suka kaddamar da mummunan harin, miyagun sun harbe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku har lahira.

Bayan sun hallaka mataimakin firinsifal din ne kuma suka kutsa dakin kwanan dalibai, inda suka yi awon gaba da dalibai mata masu yawa.

An ji yadda 'yan bindiga suka farmaki makarantar

Wata mata da ke zaune a yankin da makarantar take, Malama Murjanatu Hassan Gishiri, ta tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Litinin.

Malama Murjanatu ta bayyana cewa 'yan bindigan sun farmaki makarantar kwanan ne a cikin dare, inda suka ci karensu ba babbaka na tsawon lokaci.

Ta bayyana wannan harin a matsayin 'mummunan abu da ya jefa al'ummar yankin cikin tsananin tashin hankali da firgici tsawon wannan dare.'

A cewarta, 'yan bindigar sun zo yankin a kan babura masu yawa, kuma suna har suka gama ta'asarsu ba wanda ya iya kai dauki don suna harbi da miyagun makamai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da dan kasuwa kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP

Har yanzu dai ba a ji ta bakin hukumomin tsaro game da sace daliban makarantar Kebbi ba.
Jami'an tsaro na rundunar 'yan sanda suna gabatar da aikinsu. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

An roki gwamnati ta ceto daliban da aka sace

Mai shari kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya rahoto Malama Murjanatu a shafinsa na X, tana cewa, an harbe mataimakin shugaban makarantar har lahira lokacin da yake kokarin kare daliban daga maharan.

"Mutane na ci gaba da yi masa addu'a, Allah ya jikansa. Lallai mutuwarsa ta zama abin bakin ciki sosai, muna rokon Allah ya karbi shahadarsa, ya ba iyalansa hakuri."

Duk wani yunkuri na jin ta bakin hukumomin tsaro ya ci tura har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto.

Mazauna yankin dai sun roki gwamnati da ta gaggauta ceto wadannan dalibai da aka sace, kuma a kara tsaro a makarantu da yankunan da ke ci gaba da fuskantar hare-hare.

An sace dalibai mata a jami'ar FUD

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari a ɗakunan kwanan ɗalibai na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Sojoji da 'yan sanda sun ba hammata iska a Benue, an ji abin da ya faru

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai mata guda biyar a yayin harin da suka jkai a ɗakunan kwanan da ke a wajen makaranta.

An rahoto cewa 'yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka ƙara da cewa an cafke wani mutum ɗaya bisa zargin ba ƴan bindigan bayanai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com