ISWAP: Masu Hidimar Kasa, NYSC Sun Tsallake Rijiya da Baya a Borno

ISWAP: Masu Hidimar Kasa, NYSC Sun Tsallake Rijiya da Baya a Borno

  • Sojojin rundunar haɗin guiwa sun samu nasarar ceto matasa 74 da ke hidimar kasa da suka makale a hanyar Buratai–Kamuya a Borno
  • Matasan 36 maza da 38 mata sun tsira daga yuwuwar sace su da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a lokacin da suka makale a yankin
  • Rundunar soji ta gano lamarin ne ta hanyar kyamarar CCTV, lamarin da ya sa ta yi gaggawar kai masu dauki domin su tsira da mutuncinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Sojojin rundunar haɗin guiwa ta Operation Hadin Kai sun ceci wasu matasa 74 na hukumar kula da masu hidimar ta kasa (NYSC) daga yuwuwar afkawa hannun ‘yan ta’adda a Borno.

Rahotanni sun nuna cewa an kubutar da su ne a daren Talata, da misalin 9:05 na dare, a hanyar Buratai–Kamuya, bayan motocinsu sun lalace a wajen da 'yan ta'adda ke kai komo.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

Sojoji sun gano 'yan NYSC sun makale a Borno
Daliban 'yan NYSC da sojoji su ka kai wa agaji a Borno Hoto: @ZagaOlamaMakama
Source: Twitter

Wata majiya ta shaida wa Zagazola Makama cewa cikin waɗanda aka ceto sun hada da maza 36 da mata 38, kamar yadda ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ceto 'yan NYSC

Rahotanni sun bayyana cewa CCTV da sojoji ke amfani da shi wajen sa ido ya gano motsin wasu motoci uku da ba a yadda da su ba a yankin.

An gano da cewa ganin haka ne ya sa aka tashi sojoji su ka yi gaggawar kai agaji domin kwantar da duk wata hatsaniya da ke kokarin tashi.

A cewar majiyar:

“Da isarsu, sojojin sun tarar da matasan NYSC 74 da suka makale saboda motocinsu sun samu matsala. Nan take aka ba su kariya domin kauce wa yiwuwar sace su kamar yadda ‘yan Boko Haram ko ISWAP ke yi a yankin."

Sojoji sun kwashe 'yan NYSC

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa sojoji sun yi gaggawar raka matasan daga Maiduguri zuwa Damaturu.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Kiristoci a coci, ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, sun sace mutane

An gano 'yan NYSC a makale a Borno
Motocin da suka dauko yan hidimar kasa a Borno Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Sai dai bayan sun isa Damaturu, ba su sanar da sanar da cewa za su dauki hanya zuwa karamar hukumar Hawul ba, saboda haka ba a ba su 'yan rakiya ba.

Rahoton ya ce wannan rashin sanarwar ne ya kai su ga fadawa cikin yankin da ake kallon mai hadarin aske ne ga rayuwar matafiya.

A halin yanzu, an tabbatar da cewa matasan na samun kulawa a sansanin sojoji na Buratai, inda ake shirye-shiryen raka su wurin da za su yi hidimar kasa lafiya.

'Yar NYSC ta shiga matsala

A baya, mun wallafa cewa wata mai hidimta wa kasa, Rita Uguamaye, wacce aka fi sani da Raye, ta zargi hukumar kula da masu hidimar kasa (NYSC) da hana ta takardar kammala hidima.

Raye, wacce ta yi hidimar ƙasa a Jihar Legas, ta fara samun suna ne a watan Maris 2025 bayan wani bidiyo da ta wallafa tana sukar gwamnati kan matsin tattalin arziki da hauhawar farashi.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

A cikin bidiyon, ta kira shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu mugun shugaba, tare da caccakar gwamnatin tarayya kan jinkirin aiwatar da sabon alawus ga masu bautar ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng