Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Kara Dauko Wa Najeriya Bashin Sama da Naira Tiriliyan 1

Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Kara Dauko Wa Najeriya Bashin Sama da Naira Tiriliyan 1

  • Bola Ahmed Tinubu ya samu amincewar Majalisar Dattawa kan baukatarsa ta ciyo sabon bashi da ya kai Naira tiriliyan 1.15
  • Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu bayan nazari kan rahoton kwamitin kula da harkokin lamunin cikin gida da na waje
  • Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da kudin wajen cike gibin kasafin kudin shekarar 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta kammala muhawara kan bukatar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta sake dauko wa Najeriya bashin makudan kudi.

Shugaba Bola Tinubu ya nemi izinin Majalisar Dattawa na sake karbo lamunim Naira tiriliyan 1.15 daga kasuwar bashi ta cikin gida domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025.

Majalisar Dattawa.
Hoton zauren Majalisar Dattawa da ke Abuja Hoto: Nigeria Senate
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa bayan kammala bin duk wasu matakan doka, Majalisar Dattawa ta sahalewa shugaban kasa ya ciyo wannan bashi don ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu

Majalisar ta amince da bukatar karbo rancen ne a zamanta na yau Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025 bayan tafka muhawara kan rahoton Kwamitin Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje.

Tun farko dai majalisar ta dora wa kwamitin aikin nazari kan shirin lamuni don cike gibin kasafin kuɗin 2025, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko (APC, Sakkwato ta Arewa).

Mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu (PDP, Taraba ta Tsakiya), ne ya gabatar da rahoton a gaban sauran sanatoci yau Laraba.

A yayin gabatar da rahoton, Sanata Manu ya bayyana cewa:

“Majalisar Dattawa ta karɓa kuma ta yi nazari kan rahoton Kwamitin Lamunin Cikin Gida da Na Ƙasashen Waje don amincewa da shirin lamuni da zai taimaka wajen cike gibin kasafin kuɗin 2025.”

Tinubu zai sake karbo bashin N1.15trn

Tn da farko, a ranar 4 ga Nuwamba, Shugaba Tinubu ya rubuta wasika yana neman amincewar majalisa domin karbo rancen Naira tiriliyan 1.15 daga kasuwar lamuni ta cikin gida.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Dalilin da ya sa Amurka ba za ta saka wa Najeriya takunkumi ba

A wasikar, Shugaba Tinubu ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa wadannan kudi za su taimaka wajen aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar Shugaba Tinubu a zaman majalisa na ranar 4 ga Nuwamba, 2025.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Me yasa Tinubu zai kara ciyo bashi?

A cewar wasikar Shugaba Tinubu, za a yi amfani da kudintaimaka wajen cike gibin kuɗi da tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati da ayyuka da ke cikin kasafin kuɗin shekarar 2025.

Bayan karbar rahoton kwamiti da muhawara a tsakanin sanatoci, majalisar dattawa ta amince wa Tinubu ya karbi rancen wadannan kudade domin gudanar da ayyuka, kamar yadda Channels tv ta kawo.

An yi yunkurin tsige Sanata Akpabio

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya ce an yi yunkurin tsige shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio daga kan mukaminsa.

Sanata Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa kan sanatoci a hade yake, wanda hakan ya ba su damar dakile yunkurin sauke Akpabio daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura manyan kusoshi zuwa Landan, an fara kokarin dawo da Sanata Ekweremadu Najeriya

Ya kuma tabbatar da cewa Majalisa ta maida hankali kan yin dokokin da za su inganta rayuwar talakan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262