Bayan Mutuwar Mashood, Mai Martaba Sarki Ya Nada Sabon Babban Limamin Kasar Oyo

Bayan Mutuwar Mashood, Mai Martaba Sarki Ya Nada Sabon Babban Limamin Kasar Oyo

  • Sarki Akeem Owoade ya tabbatar da nadin Bilaal Akinola a matsayin sabon babban limamin Oyo bayan tsallake tantancewa
  • Nadinsa ya kawo ƙarshen shekaru biyu da kujerar ta kasance babu mai rike da ita bayan rasuwar Sheikh Ajokidero III
  • Oba Owoade ya nuna farin cikinsa da wannan nadin, yana mai cewa Allah ne ya ɗaukaka Bilaal zuwa matsayi mai daraja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Oyo - Alaafin na Oyo, Oba Akeem Owoade, ya nada Bilaal Akinola a matsayin sabon babban limamin kasar Oyo,

An tabbatar da wannan nadin ne a wani bikin da ya gudana ranar Talata a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Sarkin Oyo, Oba Akeem Owoade ya nada sabon babban limamin masarautar Oyo.
Hoton Bilaal Akinola, sabon babban limamin kasar Oyo. Hoto: @abdullahayofel
Source: Twitter

Aalafin ya nada sabon limamin Oyo

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na fadar Alaafin, Bode Durojaye, ya fitar, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sabon ministan jin kai ana cikin neman a biya kudin N Power

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bode Durojaye ya bayyana cewa an yi wa Bilaal Akinola nadin ne bayan ya tsallake dukkan matakan tantancewa da aka gudanar.

Wannan kujerar ta kasance babu mai rike da ita tun bayan rasuwar tsohon babban limami, Sheikh Mashood Ajokidero III, a shekarar 2023, wanda ya haifar da jinkiri da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Musulmi a yankin.

Sakon Alaafin ga sabon limami

A cikin jawabin sa, Oba Owoade ya bayyana farin cikinsa da wannan nadin, yana mai cewa Allah ne ya ɗaukaka sabon limamin zuwa matsayi mai daraja da mutunci a cikin al’ummar Oyo.

Sanarwar Durojaye ta ce:

“Oba Owoade na cike da farin ciki tare da yi wa sabon limamin addu'ar samun jagoranci da kuma rokon Allah ya rike hannayensa a wannan matsayi da ya taka.
"Bayan ya tsallake kowane gwajin tantancewa, Oba Owoade na farin cikin sanar masa da cewa ya zabe shi a matsayin sabon babban limamin Oyo."

Kara karanta wannan

Dambazau: ‘Yan ta’adda sun mamaye garuruwa, suna karɓar haraji da kafa dokoki a Arewa

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan lokaci “ya na da muhimmanci ga al’ummar Oyo da Musulmi baki daya, domin jagoranci a Musulunci yana buƙatar tawali’u, gaskiya da adalci.”

Sarkin Oyo ya ce nadin sabon limamin oyo na zuwa ne bayan tantancewa da aka gudanar.
Taswirar jihar Oyo da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tarihin sabon Babban Limami, Bilaal Akinola

Rahoton The Guardian ya nuna cewa an haifi Bilaal Akinola a ranar 15 ga Afrilu, 1965, a gidan Imam Ogunbado da ke unguwar Akeugberu a cikin ƙaramar hukumar Oyo ta Yamma, jihar Oyo.

An ce Bilaal Akinola ya karanci shari’a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya samu gogewa a ofishin Barista Niyi Badmus & Co. tsakanin 1995 zuwa 2000.

Daga bisani, ya yi aiki a Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA), wadda daga baya ta zama PHCN, inda ya riƙa kula da harkokin doka da biyan kuɗin lantarki.

Limamin Oyo, Sheikh Mashood III ya rasu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, babban limanin masarautar Oyo, Sheikh Mashood Ajokidero III, ya rigamu gidan gaskiya.

Rahoto ya nuna cewa Sheikh Mashood Ajokidero, ya rasu ne a ranar 26 ga watan Janairun 2023, lamarin da ya jefa Musulmi a yanayin kaduwa.

Kara karanta wannan

Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya

Ba a samu wasu cikakkun bayanai game da rasuwar limamin ba, amma an tabbatar da cewa an yi masa sutura kamar yadda addini ya tanada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com