‘Babu Korafi’: Gwamna Ya Fadi Yadda Suke Shanawa da Ciyamomi a Mulkin Tinubu

‘Babu Korafi’: Gwamna Ya Fadi Yadda Suke Shanawa da Ciyamomi a Mulkin Tinubu

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi magana kan yadda gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi ke mulki cikin sauki
  • Sanwo-Olu ya ce an samu ƙaruwa da kashi 62 cikin ɗari a rabon kuɗaɗen jihohi da 47 cikin ɗari ga ƙananan hukumomi
  • Sanwo-Olu ya yaba da yunƙurin Tinubu na kafa ‘yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro da kusantar da mulki ga jama’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana irin morewa da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi ke yi a yanzu.

Sanwo-Olu ya ce a mulkin Shugaba Bola Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai ƙara kuka da rashin kuɗi.

Sanwo-Olu ya yabawa salon mulkin Tinubu
Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Bola Tinubu. Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Gwamna ya fadi alherin da suke samu

Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a yayin wani babban taro na rana ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank ta shirya a 'Arewa House' a Kaduna, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce a yanzu gwamnatin tarayya ta ƙara yawan kuɗaɗen da ake rabawa jihohi da ƙananan hukumomi domin ci gaban ƙasa.

An gudanar da taron ne domin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai wanda ya haɗa shugabanni, masana, matasa da masu ruwa da tsaki a harkar ci gaban ƙasa.

A jawabinsa, Sanwo-Olu ya yaba wa ‘yan Najeriya bisa juriya duk da kalubalen da suka fuskanta, yana mai cewa gyaran tsarin kuɗi da Tinubu ya yi ya canza yanayin tattalin arzikin jihohi da ƙananan hukumomi.

Ya ce:

“A yau, labarin ya canza. Kowane gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma zai iya shaida yadda kuɗaɗen shiga suka ƙaru a zamanin Tinubu.”

Ya bayyana cewa daga 2023 zuwa 2024, rabon kuɗaɗen da ake ba jihohi ya ƙaru da kashi 62 cikin ɗari, yayin da ƙananan hukumomi suka samu ƙaruwa da kashi 47 cikin ɗari.

Ya kuma yaba da sabon tsarin haraji da ya rage rabon gwamnati daga kashi 15 zuwa 10 cikin 100, inda jihohi ke samun kashi 55, ƙananan hukumomi kuma 35 cikin 100.

Kara karanta wannan

Minista ya fadawa 'yan Najeriya abin da za su yi bayan barazanar Donald Trump

Gwamna ya fadi alherin da suke samu a mulkin Tinubu
Bola Tinubu yayin ganawa da gwamnoni a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Manufar Tinubu kan yan sandan jihohi

Gwamna Sanwo-Olu ya kara da cewa Tinubu na da niyyar kafa ‘yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro, yana mai cewa:

“Shugaban kasa yana duba batun tsaro gaba ɗaya. Dole ne a kafa ‘yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro.”

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa jihar Lagos za ta ci gaba da haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen aiwatar da ajandar Renewed Hope, cewar ThisDay.

An rushe masallaci a kasuwar Lagos

Kun ji cewa al'ummar Musulmi sun koka bayan gwamnatin Lagos ta taɓa masallaci yayin rushe-rushe cikin kasuwa wanda ya jawo asarar dukiya.

Gwamnatin Jihar Lagos ta rushe kasuwar Costain, inda ta kori ‘yan kasuwa da dama tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira.

Shaidu sun ce jami’an hukumar LASTMA da KAI sun isa wurin da rana, suka tarwatsa jama’a da hayaki mai sa hawaye kafin rushe masallaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.