Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Farmaki Motoci 5, Sun Sace Bayin Allah a Kogi
- ‘Yan bindiga sun tare motocin fasinjoji a hanyar Ayere–Kabba, jihar Kogi, sun kashe mutum ɗaya, sun sace wasu da dama
- Ganau ya ce maharan sun bude wuta kan matafiyan daga Legas zuwa Abuja, yayin da wasu suka tsira da raunukan harsashi
- Wannan na zuwa ne yayin da fadar shugaban ƙasa ta ce an samu raguwar asarar rayuka saboda harin 'yan ta'adda da 81%
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - An samu tashin hankali a hanyar Ayere–Kabba da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari kan matafiya.
An ruwaito cewa, 'yan ta'addar dauke da miyagun makamai sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu fasinjoji da dama.

Source: Original
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi bayan motocin matafiyan sun faɗa cikin tarkon 'yan ta'addar, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun farmaki motoci
Rahotanni daga al’ummar yankin sun bayyana cewa ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace ba, amma an tabbatar da cewa fasinjoji da dama sun shiga hannun ‘yan bindigar.
Wasu daga cikin matafiyan da suka tsira sun ce maharan sun buɗe wuta kan motoci da dama, ciki har da motar Camry da kuma Boxer, inda suka tafi da dukkan fasinjojin.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Kolawole Olawoye, ya shaida cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Legas lokacin da ya harin ya rutsa da shi.
“Muna tafiya daga Legas zuwa Abuja, sai muka shiga cikin tarkon 'yan bindigar a wajen Ayere. Na yi ƙoƙarin juyar da motata, amma ‘yan bindigar suka bude wuta. Harsashi ya lalata motar, muka fito muka gudu cikin daji."
- Kolawole Olawoye.
Mutum 1 ya mutu, an sace wasu da dama
Ya ƙara da cewa shi da wasu fasinjoji uku ciki har da mata sun samu raunukan harsashi, kuma daga baya mazauna yankin suka kai su asibitin Kabba.
Wadanda suka jikkata sun haɗa da Urajo Babangida, Leonard Amuze, Mercy Avine, da Babangida, yayin da mutum ɗaya ya rasu sakamakon tsananin raunukan da ya samu.
Wani ganau ya ce an samu motoci guda biyar a wajen harin, ciki har da motoci biyu masu lambar MAN 399XA da MAN 425XA, ɗaya bas da kuma ƙananan motoci biyu.
An ce 'yan ta'addar sun iza keyar matafiya da dama zuwa cikin daji, kuma har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

Source: Twitter
Gwamnati ta ce an samu tsaro a kasa
Wannan hari ya faru ne a daidai lokacin da fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an samu raguwa hare-haren 'yan ta'adda da kashi 85 daga 2015 zuwa yanzu.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na fadar shugaban kasa ranar Lahadi, gwamnati ta ce an kashe ‘yan ta’adda fiye da 13,000 cikin shekara ɗaya, yayin da masu tayar da kayar baya 124,000 suka mika wuya.
Haka kuma, sama da mutane miliyan 2.1 da suka rasa matsugunansu sun koma gidajensu ta ƙarƙashin shirin sake gina gidajen 'yan gudun hijira na gwamnatin tarayya.
Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji sun kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa da su a tsakanin yankin Buratai–Kamuya, jihar Borno.
Dakarun sojojin Najeriyar sun kuma lalata sansanin 'yan Boko Haram/ISWAP, yayin da aka kwato makamai, motoci, da kayan abinci.
Bugu da kari, an ruwaito cewa sojojin sun samu nasarar kama mutane 29 da ake zargin suna kai kayayyaki ga ‘yan ta’adda a yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


