Wasu 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Fasinjoji a Osun, Sun nemi a biya 50 Miliyan

Wasu 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Fasinjoji a Osun, Sun nemi a biya 50 Miliyan

- Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji uku a garin Osu dake kan babbar hanyar Ufe-Ilesha, jihar Osun

- An bayyana ɗaya daga cikin waɗan da suka sace da suna Usman kuma ɗan uwa ne ga Sarkin Hausawan Iyere

- Jami'an yan sanda tare da haɗin guiwar wasu mafarauta sun shiga dajin garin Osu don kuɓutar da mutanen kuma sun kamo yan bindigan

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da fasinjoji uku a garin Osu, kan babbar hanyar Ife-Ilesha, jihar Osun.

KARANTA ANAN: Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin motan hanyar Bauchi da Kano

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka sace sunan sa Usman, kuma ɗan uwa ne ga Sarkin Hausawan garin Iyere.

Sauran mutane biyun da abun ya ritsa dasu ba'a gane ko suwa ye ba.

Yan bindigan sun tafi da mutane ukun zuwa wani daji a garin na Osu, bayan sun farmaki mitar da suke ciki.

Rundunar yan sandan jihar sun haɗa gwuiwa da wasu mambobin ƙungiyar mafarauta a jihar don ganin an kuɓutar da waɗan da aka sace. Amma har yanzun basu gano su ba.

Sarkin Hausawa, Haruna Tanko, ya tabbatar da sace ɗan uwansa, amma yace bai san ko su waye sauran mutane biyun ba.

Wasu 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Fasinjoji a Osun, Sun nemi a biya 50 Miliyan
Wasu 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Fasinjoji a Osun, Sun nemi a biya 50 Miliyan Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

"Tabbas 'yan bindiga sun sace ɗan uwa na kuma sun nemi a basu kuɗin fansa, amma har yanzun bamu haɗa kuɗin ba," inji Tanko.

KARANTA ANAN: Jihar Kano da Legas na da matukar muhimmanci ga Najeriya, Inji Asiwaju Bola Tinubu

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin don an kawo musu rahoto a ofishin su.

Opalola yace:

"An kawo mana rahoton faruwar lamarin a ofishin mu na garin Osu, Tanko wanda ake kira Sarkin Hausawa ne ya kawo rahoton. Ya ce wani ya kira shi a wayar salula ya faɗa masa an sace ɗan uwansa Usman da wasu mutane biyu."

"Ya kuma bayyana mana sun nemi a biya su 50 miliyan kuɗin fansa. Jami'an mu na aiki tuƙuru don kuɓutar da waɗan da aka sace kuma su kamo yan bindigan."

A wani labarin kuma Likitoci zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba

Ƙungigar Likitocin ƙasar nan NARD ta bayyana cewa zata tsunduma cikin yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya su haƙƙokin su ba.

Ƙungiyar ta baiwa gwamnati wa'adi zuwa ƙarshen watan Maris ta yi abinda ya kamata ko su shiga yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262