Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da Sanatoci 97 Sun Goyi Bayan Kirkiro Jiha 1 a Najeriya"

Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da Sanatoci 97 Sun Goyi Bayan Kirkiro Jiha 1 a Najeriya"

  • Sanata Ned Nwoko ya ce kudirin kirkiro karin jiha daya a yankin Kudu maso Gabas na ci gaba da samun goyon baya
  • Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa a Majalisar Dattawa ya ce Shugaba Tinubu ya shirya rattaba hannu a kudirin idan ya tsallake matakan doka
  • Ya ce kwamitocin gyaran kundin tsarin mulki na Majalisar Dattawa da na Wakilai sun amince da kafa jihar domin samun daidaito

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa, ya bayyana cewa fafutukar da suke yi na ganin an kirkiro da jihar Anioma ya samu gagarumar nasara.

Sanata Nwoko ya yi ikirarin cewa kwamitocin gyaran kundin tsarin mulki na Majalisar dattawa na wakilai sun goyi bayan kudurin samar da jihar a Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Sanata Ned Nwoko.
Hoton Sanatan Delta ta Arewa, Ned Nwoko a Majalisar Dattawa Hoto: Ned Nwoko
Source: UGC

Wace jiha Tinubu ya goyi bayan kirkirowa?

The Cable ta tattaro cewa sanatan ya yi ikirarin cewa hatta shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya goyi bayan kafa jihar Anioma, inda ya ce hakan ba karamar nasara ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Nwoko ya bayyana haka ne a taron 'yan Izu Anioma Towns Union da aka gudanar a Abuja a karshen mako, inda aka ƙaddamar da bikin al’adun Anioma na farko.

Har ila yau, ya ce sanatoci 97 sun riga sun sanya hannu kan takarda da ke goyon bayan kafa jihar Anioma, abin da ya kira “matakin da bai taɓa faruwa ba a tarihin Najeriya.”

Abin kudirin kafa Anioma ya kunsa

Nwoko ya bayyana cewa kudirin da ya gabatar a majalisar dattawa, ya nemi a fitar da Anioma daga cikin gundumomi tara na yankin Delta ta Arewa, ciki har da hudu daga Aniocha da Oshimili, biyu daga Ika, da uku daga Ndokwa.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

Ya ƙara da cewa wasu al’ummomi daga maƙwabta, kamar Igbanke, sun nuna sha’awar shiga cikin sabuwar jihar Anioma idan an kirkiro, kamar yadda Daily Post ta kawo.

"Jiha daya kawai za a ƙirƙira, kuma wannan jihar ita ce Anioma,” in ji shi.

A cewarsa, kwamitin gyaran kundin tsarin mulki da ke da wakilci daga dukkan jihohi, ya amince cewa ya dace a ƙara wa yankin kudu maso gabas jiha ta shida domin ta daidaita da sauran yankuna.

Nwoko ya ce Tinubu zai sa hannu

Ya bayyana cewa shirin ya samu goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kuma Shugaba Tinubu ya nuna cewa zai rattaba hannu a kafa jihar da zarar an kammala bin matakan doka.

“Mun yi aiki matuka, mun kama kafa, tuntuɓa da tattaunawa a kowane matakai, ba abin da muka bari,” in ji Nwoko.
Shugaba Tinubu da Sanata Ned Nwoko.
Hoton Shugaba Bola Tinubu tare da Sanata Ned Nwoko a fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Ya bayyana cewa shugabanni daga Kudu maso Gabas, sarakuna da wakilai za su gana a Awka, Jihar Anambra, a karshen mako nan don amincewa da Anioma a matsayin jihar da za a kara a yankin.

Mutane za su amfana da kirkiro jihohi?

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kawo tsarin da jiragen kasa za su yi aiki a kowace jihar Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa an fara muhawa kan abubuwan da yan Najeriya za su amfana da su idan an kirkiro sababbin jihohi.

Masana da yan gwagwarmaya sun ce wannan tsari zai kawo fa’ida ga jama’a, daga karin wakilci har zuwa farfado da tattalin arziki.

A yanzu haka dai yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ne ke da mafi karancin jihohi guda biyar yayin da sauran ke da shida har zuwa sama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262