Barazanar Trump: Jigo a APC Ya Gargaɗi Ƴan Adawa Su Iya Bakinsu
- Kusa a APC ta jihar Osun, Hon. Olatunbosun Oyintiloye ya ce barazanar Shugaban Amurka, Donald abin damu wa ne ga kasa baki daya
- Oyintiloye ya kira a haɗa kai don kare ‘yancin ƙasa da yakar ta’addanci, ganin shi ne abin da ya jawo wa kasar wannan matsala
- Ya yi gargadi ga ‘yan adawa da su kula da kalamansu a wannan lokaci mai muhimmanci da ake bukatar kasa ta dunƙule
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Hon. Olatunbosun Oyintiloye, babban jigo a APC a Jihar Osun, ya ce bai kamata a yi watsi da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ga Najeriya.
Donald Trump da ke samun goyon bayan yan majalisar ƙasarsa na son ɗaukar matakin soja kan Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci, duk da Najeriya ta ƙaryata hakan.

Source: Getty Images
Daily Trust ta ruwaito Oyintiloye, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro kan jajircewarsu wajen magance rashin tsaro a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagora a APC ha shawarci ƴan Najeriya
Daily Post ta wallafa cewa Hon. Olatunbosun Oyintiloye, ya bukaci ‘yan Najeriya su kasance da haɗin kai don kare ‘yancin ƙasa, musamman a yanzu
Ya kuma yi kira ga shugabannin addini, al’umma, da siyasa da su mara wa Shugaba Tinubu baya wajen kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar.
Hon. Oyintiloye, wanda tsohon ɗan majalisa ne ya ce a wannan lokaci mai muhimmanci, ana buƙatar ‘yan Najeriya su yi watsi da bangarenci.
Ya ce ya kamata a hade wuri guda ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ba, su haɗa kai wajen goyon bayan Shugaba Tinubu.
Jigon APC ya zaburar da sojoji, yan adawa
Hon Oyintiloye ya jaddada cewa matsalolin tsaro da ake ciki ba sabon abu bane ga mulkin Tinubu, sai dai lamarin ya ya kara girmama bayan tsawon lokaci ana fama.

Source: Facebook
Ya ce:
“Dole ne mu haɗa kai a wannan lokaci. Bambancin addini ko siyasa bai dace ba a wannan lokaci; abin da muke buƙata shi ne haɗin kai da ƙarfi don kare ‘yancin ƙasa."
Oyintiloye ya ce duk addinai a ƙasar – Musulmi, Kiristoci, da sauran su – sun sha wahala daga ta’addanci da wasu matasa imani ke ƙaddamar wa jama'a.
Ya kuma yaba wa Amurka kan damuwarta game da tsaro a Najeriya, inda ya ce musayar bayanan leƙen asiri zai taimaka.
Ya kara da neman tallafin kayan aikin soja daga Amurka domin taimaka wa wajen shawo kan matsalar rashin tsaro.
Oyintiloye ya gargadi ‘yan adawa da su kula da kalamansu, ya kuma yi kira ga sababbin shugabannin sojoji da kada su gaza wajen aiki tuƙuru wajen ganin an ci karfin ta’addanci.
A kalamansa:
“Ba lokaci bane na yin siyasar adawa. Dole mu gane cewa zaman lafiyar Najeriya ita ce tushen duk buri na samun mukamai. Taimakon ƙasashen waje zai taimaka amma ba ta hanyar tura sojoji ba. Abin da Tinubu ke bukata yanzu shi ne goyon bayan kowa da kowa."

Kara karanta wannan
"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya
Amurka ta shiga matsala
A baya, mun wallafa cewa fiye da jiragen sama 10,000 a fadin Amurka sun samu jinkiri ko an soke tashinsu, lamarin da hukumomi suka bayyana a matsayin mafi muni tun bayan rufe gwamnati.
Ma’aikatar sufuri ta Amurka ta gargadi cewa wannan matsala na iya ƙara muni idan har gwamnati ta ci gaba da kasancewa a rufe saboda rashin biyan albashin ma’aikata.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka (FAA) ta bayyana cewa za ta rage yawan tashi a filayen jirage zuwa10% saboda gajiya da rashin albashin ma’aikatan kula da zirga-zirga.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

