Ana tsaka da Batun Barazanar Trump, Tinubu Ya Gana da Shugaban Kasar Saliyo a Abuja

Ana tsaka da Batun Barazanar Trump, Tinubu Ya Gana da Shugaban Kasar Saliyo a Abuja

  • Shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio ya kawo ziyara Najeriya yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan barazanar da Amurka yi
  • Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Maada Bio ya isa fadar shugaban kasa da karfe 9:00 na daren Juma'a, 7 ga watan Nuwamba, 2025
  • Duk da ba a bayyana makasudin wannan ganawa ba amma wasu majiyoyi sun ce taron zai maida hankali ne sha'anin tsaro a mambobin ECOWAS

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da takwaransa na ƙasar Saliyo, Shugaba Julius Maada Bio, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Shugaba Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock

Shugaba Julius Maada Bio ya isa fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin karfe 9:00 na dare agogon Najeriya a yau Juma'a, 7 ga watan Nuwamba, 2025.

Tinubu da shugaban Saliyo.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na kasar Saliyo, Julius Maada Bio a Aso Rock Hoto: @julius_maadabio
Source: Twitter

Tinubu ya gana da shugaban Saliyo

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa manyan jami’an gwamnati tarayyar Najeriya ne suka tarbe shi da girmamawa kafin daga bisani ya shiga ganawa da Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasar Saliyo, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) a halin yanzu, ya ziyarci Najeriya ne domin gana wa da Shugaba Tinubu.

Har kawo yanzu babu cikakken bayani kan abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna a wannan ganawa ta yau Juma'a, 7 ga watan Nuwamba, 2027.

Amma dai wasu rahotanni sun bayyana cewa ganawar ba ta rasa nasaba da batutuwan zaman lafiya da haɗin gwiwar tattalin arziki a yankin Afirka ta Yamma ba.

An tattaro cewa Shugaba Tinubu, shi ne wanda ya sauka daga shugabancin kungiyar ECOWAS, sannan ya mika wa Shugaba Julius Maada Bio.

Abubuwan da suka tattauna a Aso Rock

Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin baƙon nasa a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai da magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke fuskantar ƙasashen da ke cikin ECOWAS.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugabananni a jihohi 36 sun raba gardama tsakanin Damagum da tsagin Wike

A wani saƙo da Shugaba Maada Bio ya wallafa a shafinsa na X (watau tsohon Twitter), ya tabbatar da cewa ya samu ganawa da Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock.

"Na yi wata ganawa mai matukar muhimmanci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya a fadarsa da ke Abuja.
"A matsayina na Shugaban Ƙungiyar ECOWAS, mun tattauna kan batutuwan tsaron yankin Afirka ta Yamma.
"Haka kuma mun samu tattaunawa rkan muhimman kokari sa rawar da ECOWAS ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da tallafawa ci gaban tattalin arziki a cikin al’ ummarmu ta wannan yanki."

- Shugaba Julius Maada Bio.

Shugaban ECOWAS tare da Bola Tinubu.
Hoton shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio tare da Bola Tinubu a Aso Rock, Abuja Hoto: @Julius_MaadaBio
Source: Twitter

Tinubu ya karbi bakuncin Sarkin Musulmi

A wani labarin, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, a fadarsa da ke Abuja yau Juma'a.

Wannan ganawa na cikin jerin tattaunawa da neman shawarwari da Shugaba Tinubu ke yi da shugabannin addini da na gargajiya a Najeriya kan barazanar da Amurka ta yi.

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya raka Sarkin Musulmi zuwa wannan ganawa da aka bayyana a matsayin “mai muhimmanci."

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262