Karin Bayani: Ƴan Bindiga Sun Farmaki Dan Majalisar Neja, An Kashe Jami'an Tsaro

Karin Bayani: Ƴan Bindiga Sun Farmaki Dan Majalisar Neja, An Kashe Jami'an Tsaro

  • Majalisar wakilai ta yi Allah-wadai da harin da ’yan bindiga suka kai wa ayarin dan majalisa Jafaru Mohammed Ali
  • ’Yan majalisar sun bayyana harin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro da dama, a matsayin abin takaici matuka
  • Majalisar ta bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike, a kuma kama wadanda suka aikata laifin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Majalisar wakilai ta yi Allah-wadai da harin da aka kai kan ayarin dan majalisar Borgu da Agwara a jihar Neja, Jafaru Mohammed Ali.

Harin ya faru ne a ranar Talata, tsakanin karfe 1:00 zuwa 2:00 na rana, a hanyar Lumma–Babanna da ke cikin karamar hukumar Borgu, wacce ke da iyaka da Jamhuriyar Benin.

Majalisa ta yi martani yayin da 'yan bindiga suka kashe jami'an tsaron dan majalisar Neja
Zauren majalisar wakilai yayin da ake zaman majalisar a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

'Yan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja

Wannan yanki dai ya shahara da hare-haren ’yan bindiga da kuma ayyukan masu garkuwa da mutane, in ji rahoton jaridar Leadership..

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa, yayin da ayarin dan majalisar ke kan hanyar zuwa taron mazabarsa, ’yan bindiga suka tare su da bindigogi, inda aka kashe jami’an tsaro da dama, yayin da direbansa da wasu daga cikin hadimansa suka jikkata.

An kuma tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun lalata motocin da ke cikin ayarin, kuma sun dauki lokaci suna barin wuta kafin jami’an tsaro su iso wajen.

Martanin majalisar wakilai kan harin

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun majalisar, Hon. Akin Rotimi, ya bayyana harin a matsayin abin takaici da kuma rashin imani.

Ya ce dan majalisar yana kan hanyarsa ta zuwa wasu yankuna mazabarsa domin aiwatar da ayyukan raya kasa lokacin da aka tare su da harbe-harbe.

Rotimi ya kara da cewa majalisar ta yi matukar bakin ciki da rasuwar jami’an tsaro da suka sadaukar da rayukansu wajen kare dan majalisar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako mutum 500 da suka sace bayan Uba Sani ya dauki mataki

Majalisar ta bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike don gano wadanda suka aikata laifin da gurfanar da su a kotu, tana mai jaddada cewa ba za a lamunci irin wannan harin ba.

Majalisar wakilai ta bukaci a gaggauta kamo wadanda suka farmaki ayarin dan majalisar Neja.
Zauren majalisar wakilan tarayya da ke Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Karuwar hare-haren ’yan bindiga a Neja

Jihar Neja dai ta dade tana fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

A ranar 17 ga Satumba 2025, wasu ’yan bindiga suka kashe mutane 22 a wani harin da suka kai yayin da ake wani bikin baftisma a jihar Neja.

Haka kuma, a watan Yuni, akalla sojoji 17 suka mutu a musayar wuta da ’yan bindiga a garin Bangi, karamar hukumar Mariga.

Masu sharhi sun ce irin wadannan hare-hare na kara nuna bukatar sake fasalin dabarun tsaro da karfafa hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

'Yan bindiga sun farmaki ayarin 'yan kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe ƴan kasuwa shida yayin da suke hanyar zuwa cin kasuwar mako-mako a Katsina.

'Yan kasuwar sun baro kauyen Maidabino da nufin zuwa kasuwar Yantumaki, kwatsam suka yi gamo da yan bindiga a kan hanyarsu.

Kara karanta wannan

Barau ya yabawa sojoji kan kisan 'yan bindiga a Kano, ya mika sabuwar bukata

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa kafin jami'an tsaro su kawo dauki wajen, har yan bindigan sun kashe wasu, amma babu tabbacin ko sun sace wasu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com