Rikici tsakanin Lauya da Sheikh Gumi Ya Canja Salo, Ana Shirin Dangana wa ga Kotu

Rikici tsakanin Lauya da Sheikh Gumi Ya Canja Salo, Ana Shirin Dangana wa ga Kotu

  • Fitaccen lauya Malcolm Omirhobo ya ce bai zargi Sheikh Ahmad Gumi da ta’addanci ba, kamar yadda malamin ya yi zargi
  • Ya bayyana cewa kalamansa da ke neman gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike a kan malamin na bisa tsarin doka
  • Ya ce saboda haka, zancen Sheikh Gumi na cewa Malcolm Omirhobo ya ba shi hakuri ba ta taso ba, idan yana da jayayya ta tafi kotu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta – Shahararren lauya kuma mai rajin kare hakkin jama’a, Cif Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya mayar da martani ga Sheikh Ahmad Gumi.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya bai wa Malcolm Emokiniovo wa’adin awanni 24 ya ba shi hakuri tare da janye kalamansa kan danganta shi da ta'addanci.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Malcolm Omirhobo ya yi magana a kan umarnin Sheikh Gumi
Hoton Malcom Omirhobo da Sheikh Gumi Hoto:@MalcolmInfiniti
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X mai taken “Sheikh Gumi, ban bata maka suna ba, mu hadu a kotu,” ya musanta kiran Sheikh Gumi 'dan ta'adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauya ya kare kansa daga zargin Gumi

Omirhobo ya bayyana cewa kalaman da ya yi suna bisa tsarin dokar fadin albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayar da dama.

Ya rubuta cewa:

“Domin kore dukkanin shakku, magana ta ba ta kunshi bata suna ba, illa dai ra’ayi ne bisa hujjoji da kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022 suka halatta."

Omirhobo ya ce bai taba cewa Sheikh Gumi dan ta’adda ba, amma yana ganin ya dace hukumomin tsaro su binciki kalamansa da hulɗarsa da masu garkuwa da mutane.

Omirhobo ya ce Sheikh Gumi ya tafi kotu
Hoton fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Gumi
Source: Facebook

Ya ce a ganinsa, kalaman Gumi suna nuna goyon baya ga 'yan ta'adda da ke ta'addanci, saboda haka ya ke ganin babu laifi idan an ankarar da hukuma.

Kara karanta wannan

Janye biza: Wole Soyinka ya dura kan Trump, ya kira shi mai mulkin kama karya

Lauyan ya ce:

“Ban zargi Sheikh Gumi da ta’addanci ba. Abin da na yi kawai shi ne kiran gwamnati ta binciki kalamansa da ayyukansa da suka shafi kare ko neman sasanta wa da ‘yan ta’adda."

Lauya ya kalubalanci Sheikh Gumi

Ya kara da cewa idan Sheikh Gumi yana ganin an bata masa suna, ya kamata ya garzaya kotu maimakon yin barazana ko gargaɗi ta kafafen sada zumunta.

Omirhobbo ya ce:

“Idan Sheikh Gumi yana ganin an bata masa suna, kotu ce wurin da ya dace ya garzaya, ba yin barazana ko gargadi ba. Na tsaya kan maganata. Ba zan janye ta ba. Babu wanda ya fi doka, ko da kuwa malami ne."

Omirhobo ya jaddada cewa bai kamata a yi shiru idan wani yana kare ko neman hujjar da za ta amince da ayyukan ta’addanci ba, domin hakan yana da nasaba da tsaron kasa.

Gumi ya magantu kan sulhu da 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

Trump ya kara nuna yatsa ga Najeriya, ya ce ba za a ji da dadi ba

A baya, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya sake jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta bude hanyoyin tattaunawa da ’yan bindiga domin zaman lafiya.

A cewar malamin, tsawon shekaru ana fafutuka da amfani da karfi wajen yaki da ’yan bindiga, amma tsaro mai dorewa ba zai tabbata ba sai an bi hanyar sulhu da fahimtar juna.

Sheikh Gumi ya kawo yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Hamas a matsayin hujja cewa duk rikicin da ya kai kololuwa, tattaunawa ce kadai za ta iya zama mafita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng