'Yan Kasuwar Man fetur Sun Ce Farashi Zai Haura N1000 da Tinubu Ya Kawo Haraji

'Yan Kasuwar Man fetur Sun Ce Farashi Zai Haura N1000 da Tinubu Ya Kawo Haraji

  • Kungiyar dillalan mai ta MEMAN ta zargin gwamnatin tarayya da sanya sabon harajin 15% kan shigo da fetur don hana shigo da shi baki daya
  • Sakataren kungiyar MEMAN, Clement Isong, ya bayyana cewa wannan dabara da gwamanti ta bullo da shi zai jawo tashin farashin litar mai
  • Ya ce suna ganin idan har lamarin ya cigaba a haka, farashin litar man fetur zai kai kusan N1,000 yayin da farashin dizal zai haura N1,100

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Har yanzu ana tafka muhara da cece-kuce a kan karin harajin kashi 15 a cikin dari da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a kan shigo da man fetur.

Kungiyar dillalan mai ta Major Energies Marketers Association of Nigeria (MEMAN) ta ce wannan mataki tamkar haramta shigo da fetur ne gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Trump, gwamnatin Najeriya ta yi magana kan shari'ar 'yan ta'adda

Farashin litar mai zai tashi
Hoton mota dauke da fetur Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Sakataren kungiyar MEMAN, Clement Isong, ya bayyana hakan ne yayin wani taron yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasuwa sun koka da harajin fetur

Sakataren kungiyar MEMAN, Clement Isong ta bayyana cewa sabon tsarin harajin zai jawo tsadar litar mai da jama'a ke amfanin da shi a Najeriya.

A kalamansa:

“Harajin 15% ya yi tsauri kuma zai ƙara farashin fetur da dizal a kasuwa, zai ƙara kusan N122 a kan kowace lita ta fetur, yana iya ɗaga farashin zuwa N998 kowace lita a Legas, sannan zai kai fiye da N1,020 kowace lita a yankunan Arewa.”

Ya ce farashin dizal kuma zai iya tashi zuwa tsakanin N1,164 da N1,194 kowace lita, wanda zai ƙara nauyin sufuri da tsadar kayayyaki a ƙasar.

Kungiyar MEMAN ta nemi a tattauna

Wasikar amincewa da harajin ta fito daga ofishin shugaban ƙasa a ranar 21 ga Oktoba, inda aka umurci Ma’aikatar Shari’a, FIRS da NMDPRA su aiwatar da tsarin.

Kara karanta wannan

TUC: Yan kwadago sun taso Gwamnatin Tinubu kan shirin kakaba harajin 15% kan fetur

Shugaban FIRS, Zacch Adedeji, ya ce harajin zai daidaita farashin shigo da man a kasuwar cikin gida, tare da ƙarfafa cinikayyar man a kan Naira a maimakon Dala.

Ana neman Tinubu ya sassauta harajin fetur
Hoton Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Manufarmu ita ce ƙarfafa matatun mai na cikin gida, tabbatar da wadatar mai mai araha, da tabbatar da dorewar tattalin arziki a karkashin shirin shugaban ƙasa."

Sai dai MEMAN ta yi kira da a sake duba batun harajin, tana mai cewa kamata ya yi gwamnati ta fara gyara matatun mai huɗu da ake da su a cikin kasar nan.

Ya ce:

“A gaskiya, wannan haraji yana da yawa sosai. Ya kamata a yi amfani da wasu hanyoyi na kare masana’antun cikin gida ba tare da cutar da masu amfani da mai ba."

Tinubu ya sanya harajin man fetur

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabon harajin shigo da man fetur (PMS) da dizil (AGO) na kashi 15 cikin 100, lamarin da ake gani zai jawo matsala.

Wannan mataki ya biyo bayan amincewar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, domin aiwatar da tsarin da ke nufin tabbatar da tsaron makamashi da kuma ƙarfafa matatun mai na cikin gida.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun tsara yadda za su kawo farmaki Najeriya

An tura wasikar amincewar ga babban lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi, Shugaban hukumar haraji (FIRS), Zacch Adedeji, da kuma Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng