Gwamnatin Tinubu Ta Ware N400bn domin Wasu Manyan Ayyuka a Sassan Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Ware N400bn domin Wasu Manyan Ayyuka a Sassan Najeriya

  • Majalisar zartarwar Najeriya ta zauna a ranar Alhamis, inda ta tattauna batutuwa daban-daban domin kara samar da ayyukan ci gaban kasa
  • A zaman da aka yi wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, an amince da bayar da sababbin kwangilolin tituna da gyaran wasu tsofaffi
  • Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya gabatar da takardu 11, daga ciki ciki har da sababin ayyuka biyu da gaba dayansu za a yi a kan sama da N400bn

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta amince da bayar da kwangilar manyan ayyukan tituna da gyaran wasu tsofaffi.

A zaman da aka yi a ranar Alhamis, FEC ta amince da ayyukan da darajarsu ta kai fiye da N400bn domin inganta hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Dave Umahi ya ce an amince da gina da gyara wasu tituna
Hoton Ministan ayyuka Dave Umahi Hoto: Dave Umahi
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta amince da kwangilar tituna

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Dave Umahi ya ce ya gabatar da takardu 11 ga majalisar – takardu tara na duba tsofaffin ayyuka da aka gada, da kuma guda biyu na sababbin kwangiloli.

A cewarsa, majalisar ta amince da sashen biyu na aikin titin Lagos–Ibadan a kan kuɗi N43bn, domin gyara ɓangarorin da suka lalace da kuma kammala gadoji da hanya ƙarƙashin ƙasa.

A kalamansa:

“Haka kuma an amince da aikin Mushin–NNPC Junction–Apapa–Oshodi Expressway, wanda aka sabunta kudinsa daga N11bn zuwa N19bn saboda karin farashin kayan aiki."

Ayyukan da gwamnati ta amince da su

Ministan ya bayyana cewa an kuma amince da gina sashen uku na titin Sokoto–Badagry Superhighway, mai tsawon kilomita 162.97km daga Badagry.

Kara karanta wannan

A karshe, za a iya saka matatun man Najeriya a kasuwa domin sayar da su

Hanyar ta kuma ratsa zuwa iyakar jihar Oyo ta hanyar Ogun, kuma za a gina kowace kilomita a hanya a kan N3.39bn.

Dave Umahi ya ce za a kashe akalla N400bn
Ministan ayyukan Najeriya yayin jawabi ga manema labarai Hoto: Dave Umahi
Source: Twitter

Ayyuka da aka duba sun haɗa da titin Ilorin–Omu Aran–Egba, inda za a fara matakin farko mai tsawon kilomita 31km a kan N43bn, yayin da sauran kilomita 184 za su biyo baya idan kuɗi ya samu.

Umahi ya ce aikin titin East–West ma an sake tsara shi domin sauƙaƙa zirga-zirga da ƙara ƙarfin gadoji, inda mataki na farko zai ci N156bn.

Haka kuma, wasu jihohi sun ɗauki nauyin ayyukan titunan tarayya da ke yankunansu, domin rage wa gwamnatin tarayya nauyi da hanzarta kammalawa.

Gwamnati ta kinkomo manyan ayyuka

A baya, mun wallafa cewa majalisar zartarwar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 domin gudanar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa a sassa daban-daban na jihar.

Gwamnati ta ce wannan mataki na daga cikin aniyarta na tabbatar da ci gaban tattalin arziki da walwalar jama’a, musamman ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa.

Majalisar ta amince da fara gyaran manyan tituna a wasu muhimman sassa na jihar, tare da aikin fadada wasu gine-ginen gwamnati domin ƙara ingancin ayyukan ofisoshi da hukumomi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng