'Da Gaske ne Ana Kisan Kiyashi a Najeriya,' Jigon APC Ya Goyi bayan Donald Trump
- 'Dan siyasa, kuma babba a APC, Adamu Garba ya ce adadin mutanen da ake kashewa a Najeriya ya isa a kira shi kisan kiyashi
- Adamu Garba II ya ce a 2014 jam’iyyar APC ta taba neman taimakon Amurka kan kashe-kashen Kiristoci da ake yi a Najeriya
- 'Dan jam'iyyar ta APC ya bukaci gwamnatin Najeriya ta tattauna da Amurka kan yaki da ta’addanci maimakon karyata Donald Trump
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja — Wani jigo a jam’iyyar APC, Adamu Garba, ya goyi bayan ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump cewa ana gudanar da kisan kare dangi a Najeriya.
Adamu Garba, ya ce idan aka yi la’akari da yawan rayukan da aka rasa a hare-haren da ake kaiwa a fadin kasar, za a iya cewa lamarin ya kai matsayin kisan kiyashi.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya

Source: Twitter
“Mun taba neman taimakon Amurka” — Adamu Garba
A yayin wata tattaunawa da Trust TV a ranar Laraba, jigon na APC ya tuna cewa a shekarar 2014, lokacin da PDP ke mulki, wakilan APC sun kai ziyara Fadar White House domin neman taimako kan abin da suka kira “kisan kiyashi ga Kiristoci” bayan sace daliban Chibok.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garba ya bayyana cewa dangantakar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ba sabuwa ba ce, inda ya ambaci sayen makamai na dala miliyan 346 daga Amurka da kuma horar da sojojin Najeriya a can.
A cewarsa, Amurka tana da ikon shiga kasar da ke fama da ta’addanci bisa tsarin Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da ta’addanci.
“A cikin wannan yarjejeniya, Amurka na da hakkin da ake kira R2P, watau damar shiga wata kasa domin kawo karshen ta’addanci,” in ji Adamu Garba.
Ya ce saboda haka, ya kamata Najeriya ta nuna hadin kai ga Trump domin kawar da 'yan ta'adda, maimakon yin watsi da taimakon Amurka.
“A tattauna da Amurka cikin hikima” — Adamu Garba
Adamu Garba ya bukaci gwamnatin Najeriya ta yi amfani da diflomasiyya wajen tattaunawa da Amurka, ba wai ta karyata matsalar gaba daya ba.
Matashin ya ce:
“Za mu iya fada musu su ba mu makamai cikin kwarewa, mu kuma tabbatar musu cewa abin da ke faruwa ba wai ya tsaya kan Kiristoci ne kawai ba, har Musulmai ma suna cikin wadanda abin ya shafa."
Ya kara da cewa dubban mutane na mutuwa a kauyuka ba tare da wani ya kai masu dauki ba, yayin da ake kai musu hare-hare a lokacin da suke barci.
"Idan ka yi duba da yawan mutanen da aka kwashe tsawon lokaci ana kashewa a Najeriya, ana binsu har gida ana kashe su, me za ka kira hakan? Wannan dai kisan kiyashi ne."
- Adamu Garba.

Source: Twitter
“Kisan jama’a a Arewa ya zama ruwan dare”
Adamu Garba ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa sun hallaka dubban mutane a yankunan Arewa maso Yamma.
“Kauyuka da dama a Katsina, Sokoto, da Zamfara sun zama kufai gaba daya saboda hare-haren ‘yan bindiga,” in ji Adamu.
Ya kammala da cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta amince da gaskiyar lamarin, sannan ta nemi taimako na gaskiya wajen kare rayukan jama’a.
Kalli hirar a nan kasa:
Adamu Garba ya fadawa Tinubu halin da ake ciki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Adamu Garba, ɗan jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, ya ce akwai matsaloli a gwamnatin Bola Tinubu.
Jigon na APC ya bayyana cewa kwaɗayayyu ne suka zagaye Shugaba Bola Tinubu, inda ya yi zargin cewa suna gaya masa ƙarya a kan halin da ƴan ƙasa ke ciki.
Adamu Garba ya bayyana cewa ficewar wasu ƴan APC a Arewa bayan rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba abin mamaki ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

