Ya Ji Wuta: Tsohon Sanata Ya Mayar da N400m da Ake Tuhumarsa, Ya Roƙi Alfarma
- Rundunar ‘Yan sanda ta janye karar da ta shigar kan tsohon Sanata bayan badakalar Naira miliyan 400 da ake yi masa
- Lauyan sufetan yan sanda ya sanar da kotu cewa Andy Uba da abokin shari’arsa sun biya cikakken kudin
- Sanata Andy Uba ya wakilci mazabar Anambra ta Kudu da ke Kudancin Najeriya daga shekarar 2011 zuwa 2019
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya janye karar da ya shigar kan tsohon Sanata Andy Uba da abokinsa, Benjamin Etu.
An shigar da karar Sanata Uba ne a kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahanar Naira miliyan 400.

Source: Facebook
Lauyan IGP, Aminu Abdullahi, ya sanar da kotu cewa an cimma sulhu tsakanin bangarorin da ke rikici, inda aka biya cikakken kudin da ake tuhumarsa da shi, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta umarci a kamo Sanata Andy Uba
Hakan ya biyo bayan rundunar yan sanda ta bukaci Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta ba da umarnin kamo Sanata Andy Uba.
Kotu ta bukaci tsohon sanatan ya gurfana a gabanta ranar 28 ga watan Oktoba, 2025 ko kuma ta bayar da umarnin kama shi.
Alkalin kotun ya dauki wannan mataki ne a shari'ar da ake tuhumar Andy Uba da wani mutumi da zambar Naira miliyan 400.
A baya, Gwamnatin Tarayya ta ba da izini ga IGP ya gurfanar da Uba da Etu, inda ake tuhumar su da yin zamba da sunan samun mukamin Darakta-Janar na NDDC ga duk wanda zai biya makudan kudin.
Kotun ta ce wannan laifi ne karkashin dokar zamba da almundahana ta shekarar 2006, wanda ke iya jawo hukunci mai tsanani idan aka same su da laifi.

Source: UGC
Dalilin janye shari'ar Sanata Andy Uba

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya yaba wa sojoji bisa nasarar da suka samu a Kano, ya tura sako ga Tinubu
Majiyoyi sun ce an janye karar bisa sashe na 108(5) na dokar ACJA ta 2015 bayan tabbatar da biyan kudaden duka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Lauyan yan sanda, Abdullahi ya bayyana cewa Uba, tsohon Sanata mai wakiltar yankin Anambra ta Kudu, da abokinsa sun biya Naira miliyan 400.
Ya tabbatar da cewa an biya kudin ne ga wanda ya kai korafi, Dr. George Uboh, wanda ya tabbatar da karɓar kuɗin cikin yarjejeniyar sulhu da aka sanya hannu a kai.
Mai shari’a Mohammed Umar, bayan sauraron bangarorin biyu, ya karɓi bukatar janye karar, ya soke tuhume-tuhumen, sannan ya sallami Uba da abokinsa daga shari’ar.
An karyata cewa za a rataye tsohon gwamna
Kun ji cewa wata sanarwa da ta yadu a kafofin sadarwa ta yi ikirarin cewa za a yanke wa tsohon gwamnan hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan zargin cin hanci.
Majiyar ta ce ana zargin tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu da badakalar N1trn wanda ya jawo yanke masa hukuncin kafin daga bisani a karyata labarin.
Binciken kwa-kwaf ya nuna wannan labari ƙarya ne, babu wani alkalin kotu mai suna Chukwuemeka Nwogu da ya yanke hukuncin kamar yadda ake yadawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
