Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Ministoci, Ya Sha Alwashi kan Ta'addanci

Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Ministoci, Ya Sha Alwashi kan Ta'addanci

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin minisotoci guda biyu da suka bar gwamnatinsa saboda dalilai daban-daban
  • Mai girma Bola Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci guda biyu wadanda suka fito daga jihohin Plateau da Enugu
  • A yayin rantsar da ministocin, shugaban kasan ya yi tsokaci kan kokarin da gwamnatinsa ke yi na murkushe ta'addanci a Najeriya

Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci guda biyu.

Shugaba Tinubu ya rantsar da Dr. Bernard Mohammed Doro da Kingsley Tochukwu Udeh (SAN) a matsayin ministoci a tarayyar Najeriya.

Shugaba Tinubu ya sha alwashi kan ta'addanci
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Tinubu ya rantsar da ministocin ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Nuwamba yayin taron majalisar zartarwa ta kasa (FEC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya rantsar da ministoci

Dr. Bernard Doro ne ya maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi makonni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta tantance mutumin da Shugaba Tinubu zai nada a matsayin Minista

A nasa ɓangaren, Barrister Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda majalisar dattawa ta tabbatar a ranar Alhamis, ya maye gurbin tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji.

Uche Nnaji dai ya yi murabus ne bayan an zarge shi da yin amfani da takardun bogi.

An rantsar da ministocin ne kafin fara taron FEC a zauren majalisar zartarwa da ke fadar shugaban kasa da ke Abuja, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Tun da farko ministan kuɗi Wale Edun, ya gabatar da rahoto game da ci gaban tattalin arzikin kasa.

Me Tinubu ya ce kan ta'addanci?

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa duk da girman aikin da gwamnatinsa ta sa a gaba, ana gudanar da muhimman ayyuka kuma gwamnati za ta yi nasara wajen murƙushe ta’addanci.

Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa na tattaunawa ta fuskar diflomasiyya da sauran kasashen duniya.

“Abu mafi muhimmanci shi ne cewa, duk da kalubalen siyasa da muke fuskanta, za mu ci gaba da hulɗa da abokanmu na ƙasashen waje."
"Aikin da ke gaba babba ne, amma muna tattaunawa da duniya ta hanyar diflomasiyya. Za mu shawo kan ta’addanci a kasar nan.”

Kara karanta wannan

Majalisa ta dakatar da shirin tantance sabon ministan Tinubu, an ji dalili

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Manyan jami'ai sun je taron FEC

Daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron akwai:

  • Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume
  • Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Esther Didi Walson-Jack
  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu
  • Ministoci da mashawarta na musamman ga shugaban kasa

Majalisa ta dakatar da tantance minista

A wani labarin kafin nan, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da tantance sabon ministan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada.

Majalisar dattawan ta dakatar da tantance ministan ne saboda rashin gabatar da rahoton hukumomin tsaro a kansa da ba a yi.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa ba za a ci gaba da tantance ministan ba har sai an gabatar da rahoton.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng