Bayan Barazanar Trump, Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana kan Shari'ar 'Yan Ta'adda
- Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana dalilin da ya sa aka samu tsaiko a kan shari'ar da ake yi da 'yan ta'addan Ansaru a kasar nan
- Hukumar ta ce matsalolin doka da tsarin shari’a ne suka jawo jinkirin shari’ar masu hannu a harin ginin Majalisar Ɗinkin Duniya da ya faru a 2011
- Ta ce tana ci gaba da gurfanar da shugabannin kungiyar Ansaru da wadanda ake zargi da kai harin cocin Owo da kuma kisan Yelwata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana dalilin da ya sa ake samun jinkiri wajen gurfanar da wadanda da kai hari a kan ginin Majalisar Ɗinkin Duniya a 2011.
Hukumar ta ce duk da wadanda aka ake zargi da aikata laifin suna hannu, an samu tsaikon shari'a ne saboda matsalolin doka da kuma tsarin gudanar da shari’a.

Kara karanta wannan
Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa Favour Dozie, Mataimakiyar darekta ta sashen hulda da jama’a na DSS, ya ce wasu lokutan ana kawo wadanda ake tuhuma kotu ba tare da lauyoyinsu sun bayyana ba.
Gwamnati ta yi bayanin shari'a da 'yan Ansaru
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Khalid Al-Barnawi, wanda ake zargin shine kwamandan kungiyar Ansaru, yana fuskantar shari’a tare da wasu mutum hudu.
Mutanen sun hada da Mohammed Bashir Saleh, Umar Mohammed Bello wanda aka fi sani da Datti, Mohammed Salisu, da Yakubu Nuhu wanda ake kira Bello Maishayi.

Source: Facebook
An kama Al-Barnawi a Lokoja, jihar Kogi, a watan Afrilu 2016, shekaru biyar bayan harin da ya kashe mutane fiye da 20 tare da jikkata wasu sama da 70.
Kotun babban tarayya karkashin alkali Emeka Nwite ta bayar da umarnin ci gaba da shari’a cikin gaggawa, inda a watan Oktoba aka nuna bidiyon wanda ake zargi ya tabbatar da aikata laifin.

Kara karanta wannan
'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Hukumar DSS na shari'a da 'yan Ansaru
DSS ta kara da cewa tana ci gaba da gurfanar da wasu shugabannin kungiyar Ansaru da ke da alaka da Al-Qaeda da suka hada da Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da mataimakinsa Mahmud al-Nigeri.
An gurfanar da su a ranar 11 ga Satumba bisa tuhuma 32 da suka shafi ta’addanci, inda aka shirya ci gaba da shari’ar a ranar 19 ga Nuwamba.
Haka kuma, hukumar ta ce tana shari’a da wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a harin cocin Katolika na St. Francis da ke Owo, jihar Ondo.
Harin, wanda ya faru a ranar 5 ga Yuni, 2022, ya kashe mutum fiye da 40 kuma ya jikkata sama da 100. Kotun ta ki bayar da belin wadanda ake tuhuma.
A wani bangare, DSS tana gurfanar da wasu da ake zargi da hannu a kisan gilla na Yelwata da ya faru a karamar hukumar Guma ta jihar Binuwai a ranar 13 ga Yuni, 2025.
Trump ya kara gargadi ga Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara yin maganganu masu ƙarfi kan yiwuwar tura sojoji ko amfani da jiragen sama a Najeriya sakamakon zargin kisan Kiristoci.
A ranar 31 ga watan Oktoba, 2025 ya mayar da Najeriya ƙasa mai matsala ta musamman saboda ƙarancin matakan gwamnati na ƙin dakile kashe-kashen jama’ar Kirista.
A cikin wani bidiyo da ya saki a kafofin sada zumunta, Trump ya gargadi gwamnatin Najeriyar da ta gaggauta daukar mataki, ya kuma bayyana cewa Amurka za ta dakatar da tallafi ga kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
