Majalisar Dattawa Ta Tantance Mutumin da Shugaba Tinubu Zai Nada a matsayin Minista

Majalisar Dattawa Ta Tantance Mutumin da Shugaba Tinubu Zai Nada a matsayin Minista

  • Majalisar Dattawa ta samu rahoton tsaro kan wanda Bola Tinubu yake so ya nada minista daga Enugu, Kingsley Udeh (SAN)
  • A zaman ta na ranar Alhamis, Majalisar ta amince da nadin Udeh bayan ya amsa tambayoyi daban-daban daga sanatoci
  • Udeh, zai maye gurbin Uche Nnaji, wanda ya yi murabus a watan jiya saboda zargin da ake yi masa na amfani da takardun bogi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da nadin Kingsley Udeh (SAN) a matsayin minista a zamanta na yau Alhamis a Abuja.

Wannan ya biyo bayan bukatar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar wa majalisar dattawa a ranar Talata, inda ya nemi a tabbatar da Udeh a matsayin minista.

Majalisar dattawa.
Hoton Majalisar Dattawa yayin da take gudanar da zama karkashin Sanata Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar Bola Tinubu ta nadin minista a zaman ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin nada Udeh a matsayin minista

Shugaba Tinubu ya nada Udeh ne biyo bayan murabus din tsohon ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha, Uche Nnaji, wanda ya ajiye mukaminsa a watan jiya.

Nnaji ya yi murabus saboda ce-ce-ku-ce da ya barke kan zargin da ake yi masa na amfani takardun bogi, musamman takardar kammala digiri da ya samu daga Jami’ar Najeriya, Nsukka.

Nnaji, wanda shi ne kadai minista daga Jihar Enugu, ya yi murabus bayan matsin lamba daga jama’a da kiraye-kirayen neman a maye gurbinsa.

Sai murabus dinsa ya sa jihar Enugu ta zama ba ta da wakilci a majalisar zartarwa ta kasa, kafin yanzu da Tinubu ya dauko Kingsley Udeh (SAN).

Bayan karanta wasikar Tinubu, Akpabio ya mika sunan Udeh ga babban Kwamitin Majalisar Dattawa domin gudanar da tantancewa da kuma bayar da rahoto.

Majalisar Dattawa ta amince da nadin Udeh

A zaman da ta gudanar ranar Alhamis, majalisar ta dakatar da wasu dokokinta domin ba da dama ga wasu manyan baƙi su shiga zauren don halartar tantancewar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dakatar da shirin tantance sabon ministan Tinubu, an ji dalili

Udeh ya shiga zauren tare da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Majalisar Dattawa, Sanata Basheer Lado, in ji rahoton Leadership

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Hoton shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabi yana jagorantar zaman Majalisa Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Akpabio ya bayyana cewa sun dage tantance Udeh daga ranar Laraba ba ne saboda ba a samu cikakken rahoton tsaro a kansa ba.

Ya ce rahoton tsaron ya iso ne da yammacin ranar Laraba kuma ya nuna cewa Udeh ba shi da wani tarihin laifi.

Bayan dan takaitattun tambayoyi daga ‘yan majalisa, an bukaci Udeh da ya miƙe ya fita daga zauren, kuma nan take majalisar ta tabbatar da shi a matsayin sabon ministan daga Jihar Enugu.

Majalisa ta gano asarar da Najeriya ta yi

A wani labarin, kun ji cewa kwamitin da majalisar dattawa ta kafa don binciken satar mai ya fara gabatar da rahoton abubuwan da ya gano.

Shugaban kwamitin, Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa binciken da suka gudanar zuwa yanzu ya nuna babbar asarar kudaden shiga da ta haura dala biliyan 300.

Ya ce an yi asarar wadannan makudan kudi ke sakamakon fitar da danyen mai ba tare an rubuta ko shigar da shi cikin lissafin kudin shigar gwamnati ba a Neja Delta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262