Zargin Kisan Kiristoci: An Gano Abin da Ya Tsonewa Trump Ido a kan Najeriya
- Masani a fannin siyasa, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce ba haka kawai Shugaba Donald Trump na Amurka ke barazana ga Najeriya ba
- Ya bayyana cewa duk wadannan kalamai na Trump da suka hada da barazana ga Najeriya ba wani abu ba ne illa siyasa ce da takaici
- Farfesa Jibrin ya ce matsalar na da nasaba da yadda Amurka ke ganin haɗin gwiwar Najeriya da China tana ƙara ƙarfafa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Farfesa Jibrin Ibrahim, masani a fannin siyasa kuma babban jami’i a cibiyar Centre for Democracy and Development (CDD), ya fadi abubuwna da suka tunzura Shugaban Amurka, Donald Trump.
Farfesa Jibrin Ibrahim ya bayyana cewa barazanar shugaban Amurka Donald Trump na kai hari ga Najeriya son zuciya ne kawai da neman wata bukata ta siyasa.

Source: Twitter
Ya bayyana haka a wata tattaunawa da Arise News a ranar Litinin, inda ya ce sabon matsin lambar da Amurka ke yi wa Najeriya yana da nasaba da siyasar duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masani: An dade da korafi a kan Najeriya
Farfesa Jibrin Ibrahim ya kara da cewa Shugaba Trump na takaicin yadda Najeriya ke ƙara yin hulɗa da China.
A kalamansa:
“Gwamnati na sane da irin waɗannan korafe-korafe daga hukumar addinai ta Amurka. Amma matsalar ita ce, gwamnati ba ta taɓa mayar da martani kai tsaye ba, don haka labarin kisan Kiristoci ya dade yana yawo a Washington."

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa a wani lokaci ma, an yi zaman sauraron ƙorafe-ƙorafe a majalisar dokokin Amurka, amma ofishin jakadancin Najeriya bai je ba.
Ya ce:
“Lokacin da ƙasarka ta yi shiru, sukan adana waɗannan takardu, su fito da su idan suna son nuna fushi a kan wani abu."
An gano dalilin matsin lambar Trump
Farfesa Ibrahim Jibrin ya bayyana cewa barazanar Trump ta zo ne a lokacin da Najeriya ta rattaba manyan yarjejeniyoyi da China.
Ya ce an shiga wadannan yarjeniyoyi a bangarorin masana’antu, ma’adinai da tashoshin jiragen ruwa, kuma abin bai yi wa Amurka dadi ba.
Farfesa Jibrin ya ce:
“Wannan ne dalilin da ya sa suke farfado da tsofaffin ƙorafe-ƙorafe domin tsoratar da Najeriya."
Ya ce kididdigar Amurka kanta ta nuna cewa kashe-kashen a Najeriya ba na Kiristoci kaɗai ba ne, domin fiye da mutane 2,000 an kashe su a masallatai, yayin da 1,800 aka kashe a coci-coci.
Game da barazanar kai farmaki, Farfesan ya ce:
“Ba su da niyyar shiga yaƙi da ƙananan ‘yan ta’adda masu babura a dazuka. Tsawon shekaru 50, Amurka ba ta taɓa cin nasarar yaƙi da ƙungiyoyi irin wannan ba.”
An shawarci Tinubu kan Trump
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya shawarci Bola Tinubu da ya tattaro tsofaffin shugabanni domin tattaunawa kan barazanar Donald Trump ga Najeriya.
Sule Lamido ya ce haɗin kan manyan shugabanni zai ba Najeriya damar kare ‘yancinta da kuma kiyaye mutuncinta a duk wata mu’amala ta ƙasa da ƙasa domin kawar da barazana.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa tattaunawa da tsofaffin shugabannin zai taimaka wa da gwamnati mai ci wajen sanin yadda ya dace ta bullowa al'amarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


