CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa Barazanar Trump na Kawo Farmaki a Najeriya

CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa Barazanar Trump na Kawo Farmaki a Najeriya

  • Barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ta kawo farmaki na ci gaba da daukar hankula
  • Kungiyar CAN ta reshen jihohin Arewacin Najeriya ta yi tsokaci kan kalaman na shugaban kasar Amurka
  • Shugaban kungiyar ya bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su sanya idon basira wajen kallon kalaman na Trump tare da fassara su yadda ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya ta Arewa (CAN) a jihohi 19 da Abuja ta yi tsokaci kan barazanar da Donald Trump, ya yi ta kawo hari a kasar nan.

CAN ta bukaci Kiristoci da Musulmai su yi amfani da kalaman Trump, kan zargin kisan gillar Kiristoci a Najeriya, a matsayin kiran hadin kai da aiki tare don kawo karshen kisan mutane da rashin jituwa ta addini a kasar.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

Fasto John Hayab ya yi martani kan kalaman Trump
Shugaban CAN a Arewa da Shugaba Donald Trump Hoto: Joseph John Hayab, Donald Trump
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce shugaban kungiyar, Fasto John Hayab, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me CAN ta ce kan kalaman Trump?

Ya ce maimakon daukar maganganun Trump a matsayin masu kawo rarrabuwar kai, ya bukaci 'yan Najeriya su gansu a matsayin dama ta haɗin kai domin kawo karshen kashe-kashe da rikice-rikicen addini da ke addabar kasar.

Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci a Najeriya suna fuskantar zalunci, tare da jawo hankalin duniya kan lamarin.

Fasto John Hayab ya ce, ya kamata kalaman Trump su zama karatun ta-natsu ga mabiya addinai domin su nemi gwamnati ta dauki matakan tabbatar da tsaron rayuka da ‘yancin ibada ga kowa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

“Ya kamata mu dauki maganar Trump game da kisan gillar Kiristoci a Najeriya a matsayin damar hadin kai tsakanin Kiristoci da Musulmai masu son zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Wike ya zargi 'yan adawa da wuce gona da iri wurin yada karya

"Domin su matsa wa gwamnati lamba ta dauki mataki na gaskiya wajen kawo karshen kisan kowane mutum saboda addininsa ko asalinsa."

- Fasto John Hayab

Ya ce, idan aka kalli kalaman Trump cikin natsuwa da adalci, za a ga damuwa ce ba zargi ba, kuma sautin muryar bako ne mai nuna kulawa da son ganin zaman lafiya a Najeriya, rahoton Daily Post ya zo da labarin.

“Idan mutum ya karanta kalaman Shugaba Trump da zuciya daya, zai fahimci cewa muryar bako ce da ke nuna damuwa, yana kuma kira gare mu mu yi wani abu mai muhimmanci don mu samu zaman lafiya da haɗin kai a kasarmu."

- Fasto John Hayab

Shugaban CAN ya ba 'yan Najeriya shawara
Shugaban CAN a Arewacin Najeriya, Fasto John Hayab Hoto: Joseph John Hayab
Source: Facebook

Shugaban CAN ya ja kunnen 'yan Najeriya

Fasto John Hayab ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su yi watsi da masu neman rikici da suka juya maganar domin tada husuma tsakanin mabiya addinai.

“Ya ce, idan ba a dauki mataki ba, rundunar sojojinsa za ta farmaki 'yan ta'adda ba ‘yan Najeriya ba. Ko dai wasu daga cikinmu sun amince cewa suna daga cikin ‘yan ta’addan ne?”

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

- Fasto John Hayab

Faston ya jaddada cewa abin da ‘yan Najeriya ke nema shi ne ‘yanci ga kowa ya gudanar da addininsa cikin walwala da tsaro.

“Abin da muke so shi ne ‘yanci ga kowa don yin ibada yadda yake so, ko Kirista ne, Musulmi ne, ko kuma mai tunani daban."

- Fasto John Hayab

Wike ya magantu kan kalaman Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana ra'ayinsa kan kalaman Shugaba Donald Trump.

Wike ya bayyana cewa a shirye ya goyi bayan duk mai son taimakawa Najeriya wajen magance matsalar ta'addanci.

Ministan ya ce yana maraba da duk wata irin haɗin gwiwar kasa da kasa da za ta karfafa yakin da Najeriya ke yi da ta’addanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng