Mohammed Ma'aji: Abubuwa game da Sojan da Ya Kitsa Kifar da Gwanatin Tinubu
- Ana zargin babban sojan Najeriya, Kanal Mohammed Ma’aji, shi ne wanda ya shirya yunkurin kifar da gwamnatin Najeriya
- Duk da cewa an binciki gidajensa da asusun bankinsa bayan jami'an tsaro sun kama shi, an ce Ma'aji ya ki cewa komai
- Sojan ya taba zama babban na hannun damar tsohon gwamna, Timi Sylva, wanda shi ma aka binciki gidajensa na Abuja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayelsa - An samu sababbin bayanai game da Kanal Mohammed Ma’aji, daya daga cikin manyan sojojin Najeriya da ake zargi da juyin mulki.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa, Mohammed Ma'aji na daya daga cikin sojoji 16 da ake zargin sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Source: UGC
Ma'aji: Sojan da ake zargi da juyin mulki
Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa, Kanal Ma'aji ya taɓa zama mai ba Timi Sylva shawara kan tsaro a lokacin zaben gwamnan Bayelsa na 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun shaida cewa Ma’aji, wanda ya jagoranci tsaron kamfen ɗin Sylva, ya taka “muhimmiyar rawa” wajen daukar ƙananan sojoji da kuma tsara dabarun samun kuɗi da kayan aiki.
An yi zargin cewa yana da alaƙa da wasu manyan ‘yan siyasa da suka taimaka masa, duk da cewa babu hujja kai tsaye da ta nuna hakan a yanzu.
Lokacin da aka sanya sunan Kanal Ma'aji a wadanda ake zargi, rahoto ya nuna cewa sai da jami'an tsaro suka binciki gidajen Timi Sylva a Abuja, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.
Sylva ya musanta hannu a juyin mulki
A martaninsa, Julius Bokoru, mai taimakawa Sylva kan harkokin yada labarai, ya musanta duk wata alaƙa tsakanin tsohon ministan mai da yunkurin juyin mulkin.
Jaridar Punch ta rahoto Bokoru, a cikin wata sanarwa yana cewa:
“Cif Timipre Sylva masoyin dimokuradiyya ne na hakika. Yana tare da Shugaba Bola Tinubu kuma yana marawa tsarin mulkin dimokuradiyya baya.”
Sylva, wanda ya yi mulkin Bayelsa daga 2007 zuwa 2012 a karkashin PDP, daga baya ya koma jam’iyyar APC, ya tsaya takarar gwamna a 2015 amma ya sha kaye hannun Seriake Dickson na PDP.

Source: Facebook
Ma’aji ya ki ba masu bincike hadin-kai
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa Ma’aji bai yi magana ba tun bayan kama shi, sai dai wasu ƙananan hafsoshin da ya dauka sun riga sun bayar da bayanai masu muhimmanci.
Masu binciken sun yi binciken kwakwaf a gidansa na Abuja da kuma asusun bankinsa, inda aka gano wasu kadarori da muhimman bayanai.
An haifi Ma’aji a 1976 a jihar Neja, ya fito daga kabilar Nupe, kamar yadda rahoton jaridar Premium Times ya nuna.
Ya yi karatu a Kwalejin Sojoji ta NDA, kuma ya zama kanal din soja a 2017 bayan kammala karatun dabarun tsaro da shugabanci a NIPSS, Kuru, jihar Plateau.
Ya taba zama kwamandan bataliya ta 19 a Okitipupa, jihar Ondo, daga nan aka tura shi Warri ta Arewa, jihar Delta, sannan daga baya ya shugabanci Operation Delta Safe a 2021.
Har yanzu masu binciken soja na ci gaba da bincike kan rawar da ya taka a yunkurin juyin mulkin, yayin da ake zargin akwai hannun wasu ‘yan siyasa a bayan lamarin.

Kara karanta wannan
Sanatan Amurka ya taso Najeriya, zai gabatar da kudirin hana shari'ar musulunci da batanci
An gano biliyoyi a asusun wani Kanal
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar leken asirin sojoji na ci gaba da samun nasara a binciken da take game da zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Hukumar ta gano sama da Naira biliyan 11 a asusun wani kanal da ake tsare da shi kan zargin hannu a yunkurin juyin mulki tare da wasu manyan hafsoshin soja.
Rahoto ya nuna cewa Kanal din ya taba aiki kai tsaye a karkashin wani babban hafsa da shi ma ake bincike, sannan an ce ya taba aiki a yankin Neja-Delta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

