Kwankwaso Ya Burge Fadar Shugaban Kasa bayan Sukar Donald Trump da Kira ga Tinubu

Kwankwaso Ya Burge Fadar Shugaban Kasa bayan Sukar Donald Trump da Kira ga Tinubu

  • Fadar shugaban kasa ta yaba wa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa sukar barazanar Donald Trump ga Najeriya
  • Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Kwankwaso a matsayin mai kishin kasa, yana kira ga sauran ‘yan adawa su bi sahunsa
  • Tsohon 'dan takaran shugaban kasar ya ce kalaman Trump na iya haddasa rikicin addini da kuma kara tabarbarewar tsaro a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Fadar shugaban kasa ta nuna godiya ga tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso.

Fadar Shugaban kasar ta jinjina masa saboda tsayuwarsa wajen kare martabar Najeriya daga kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump.

Fadar Shugaban Kasa ta jinjinawa Kwankwaso
Hoton Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto:@aonanuga1956
Source: Twitter

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Martanin wasu manyan Arewa kan barazanar Trump ta kai farmaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa matsayin da Kwankwaso ya dauka ya nuna kishin kasa da jajircewa wajen kare ikon Najeriya daga waje.

Fadar Shugaban kasa ta yabi Kwankwaso

Fadar Shugaban kasar nan ta bayyana jin dadin yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso bayan ya caccaki Shugaban Amurka, Donald Trump.

A sakon da ya fitar, ya bayyana cewa:

“Mun gode, Sanata Kwankwaso, saboda kishin kasa da ka nuna. Wannan lokaci ne da dukkannin shugabannin siyasa, ba tare da la’akari da jam’iyyunsu ba, su hada kai su kare kasar mu daga barazana daga 'kasashen waje."
Fadar shugaban kasa ta nemi a yi koyi da Kwankwaso
Hoton Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya ce lokaci ne da ya dace ‘yan adawa da gwamnati su ajiye siyasa a gefe, su yi amfani da murya guda wajen kare kima da mutuncin kasa.

Sanarwar ta kara da Najeriya kasa ce mai ‘yancin kai, kuma lokaci ne da za a hada kai wajen tabbatar da kawo tsaron rayuka.

Sakon Kwankwaso ga shugaba Trump

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya shawarci Tinubu ya tattaro tsofaffin shugabannin kasa kan barazanar Trump

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fitar da wata sanarwa inda ya soki kalaman Shugaba Trump, wanda ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya tura dakarunta zuwa Najeriya.

Kwankwaso ya ce irin wadannan kalamai suna da hadari, domin za su iya tada rikicin addini da lalata zaman lafiya a kasa.

A kalamansa:

“Kalaman Trump na iya rura wutar rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci a Najeriya, kuma hakan zai kara dagula matsalar tsaro."

Ya kuma yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Najeriya wajen inganta tsaro ta hanyar bata fasaha da horo maimakon yin barazanar kawo mata hari.

Buratai ya mika sako ga Trump

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon Hafsan Sojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya yi kira ga Amurka da ta sauya salon mu’amalarta da Najeriya kan zargin kiristoci.

Laftanan Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa tun asali, babu wani batu na cewa ana ware kiristoci domin yi masu kisan kare dangi saboda addininsu a dukkanin sassan Najeriya.

Tsohon hafsan tsaron ya shawarci Donald Trump da Amurka da su ajiya batun amfani da karfi da barazana zuwa amfani da tsarin haɗin kai da diflomasiyya da kowa zai mora.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Kwankwaso ya magantu kan lamarin, ya shawarci gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng