Sheikh Gumi Ya Fusata da Barazanar Amurka, Ya ba Tinubu Satar Amsa

Sheikh Gumi Ya Fusata da Barazanar Amurka, Ya ba Tinubu Satar Amsa

  • Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara bayan barazanar kasar Amurka
  • Gumi ya bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan barazanar Donald Trump ga Najeriya, yana kiran hakan cin mutunci
  • Gumi ya ce Najeriya na da sauran zabin bunkasar tattalin arziki da hadin kan soja, ba lallai ta dogara da Amurka ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi, ya yi magana kan barazanar da Amurka ta yi wa Najeriya.

Sheikh Gumi ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dauki matakin gaggawa kan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

Gumi ya ba Tinubu shaara bayan barazanar Amurka
Sheikh Ahmad Gumi da Bola Tinubu. Hoto: Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi 2 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Kwankwaso ya magantu kan lamarin, ya shawarci gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar da Amurka ta yi wa Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan barazanar da Donald Trump ya ya yi na kai farmaki a Najeriya game da zargin kisan Kiristoci.

Trump ya ba Najeriya zabi da cewa dole ta yi gaggawar kawo karshen hare-haren da ake kai wa ko kuma ya dauki mataki kan kasar.

Hakan ya jawo martani da dama daga bangarorin kasar yayin da masana ke cewa wannan barazana ba alheri ba ne ga kasar.

Abin da Gumi ya ce kan barazanar Amurka

Gumi ya bayyana maganganun Trump a matsayin cin mutunci da kuma ikon Najeriya da rashin girmamawa ga kasar wanda ya zubar mata da kima.

Ya ce bai kamata gwamnati ta yi shiru ba kan wannan kalamai masu tayar da hankali saboda girmansu.

Sheikh Gumi ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kira jakadan Amurka domin neman karin bayani da neman janye kalaman, yana mai jan kunne cewa rashin daukar mataki ya kamata ya kai ga yanke hulda da gwamnatin Trump.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya

Sheikh ya caccaki matakin da Amurka ke shirin dauka kan Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Twitter

Barazanar Amurka: Shawarar da Gumi ya ba Tinubu

Malam Gumi ya ce Najeriya ba za ta lamunci irin wannan take hakkin kasa ba duba da cewa ita ma tana da yancin kanta.

A cewarsa:

"Trump ya yi barazanar kai farmaki kan ƙasa mai cin gashin kanta babban raini ne ga ikonmu, amma za mu iya ɗaga kai mu wuce wannan.
"Shugaba Tinubu ya kira jakadan Amurka nan take; su janye barazanar ko kuma mu katse hulda da wannan gwamnati marar kan gado, akwai sauran zabin da dama don faɗaɗa tattalin arziƙi da haɗin gwiwar soja.”

Malamin ya ce akwai sauran kasashe da dama da Najeriya za ta iya dogaro da su wajen bunkasa tattalin arziki da kuma hadin kan tsaro, ba wai Amurka kadai ba.

Ya jaddada cewa Najeriya kasa mai cikakken iko ce kuma ba za ta bari a tauye martabarta ba.

Barazanar Trump: Kwankwaso ya ba Tinubu shawara

Kara karanta wannan

Lauya a Amurka ya saba da Trump kan barazana ga Najeriya, ya fadi ciwon da ke damunsa

Kun ji cewa Sanata Rabi'u Kwankwaso ya nuna damuwa kan maganganun Donald Trump game da Najeriya bayan zargin kisan Kiristoci.

Jagoran Kwankwasiyya ya jaddada cewa Najeriya tana da ’yancin kai tare da kalubalen tsaro daban-daban.

Ya ce matsalolin tsaro ba su bambanta addini ko kabila, yana rokon Amurka ta ba Najeriya fasahar yaki da ’yan bindiga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.