Zargin Juyin Mulki: Bincike Ya Gano Biliyoyi a Asusun Bankin Wani ‘Kanal’
- Hukumar leken asiri ta gano biliyoyin Naira a asusun banki na wani kanal a Najeriya da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki
- Rahotanni sun ce an fara sa ido tun August 2024, inda wadanda ake zargi suka yi ganawa a Birtaniya da Turkiyya, tare da shirya kai hari
- Ana ikirarin cewa an cire hafsoshin tsaro gaba daya ne domin boye mataki kan zargin sakaci da fallasa kamun jami’an soja 16 ga jama’a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar leken asirin sojoji na ci gaba da samun nasara a binciken da take musamman game da zargin yunkurin juyin mulki.
Hukumar ta gano sama da Naira biliyan 11 a asusun wani kanal da ake tsare da shi kan zargin hannu a yunkurin juyin mulki tare da wasu manyan hafsoshin soja.

Kara karanta wannan
Kano: 'Yan bindiga sun hallaka mutane bayan sace da dama, an 'gano' inda suka fito

Source: Twitter
Juyin mulki: An samu biliyoyi a asusun kanal
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa gano kudaden ya kara tabbatar da shakku kan rawar da jami’in ya taka a shirin kifar da gwamnati, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoto ya nuna cewa kolonel din ya taba aiki kai tsaye a karkashin wani babban hafsa da shi ma ake bincike, sannan an ce ya taba aiki a yankin Neja-Delta.
A lokacin binciken, jami’in ya yi ikirarin cewa kudaden mallakar tsohon gwamna ne wanda ya ce abokin kasuwancinsa ne.
Ya dage cewa kudin da ake magana a kai an samar da shi ne domin harkar kasuwanci ba don wani abu na sabawa doka ba.
Binciken dai ya fara tun bayan samun bayanan sirri a watan Agusta 2024, cewa akwai wasu hafsoshin soji da ke shirin hambarar da gwamnati.

Source: Facebook
Juyin mulki: adda aka tsara kai hare-haren
Majiyoyi sun ce an fara bibiyar tattaunawa, kudade, da hulda da kasashen waje tun kafin kama kowa.
An ce wadanda ake zargi sun tsara kai hari sau uku, ranar dimukradiyya a 2025, da 1 ga watan Oktoba, amma hukumar leken asirin ta rigasu ta san matakansu.
Haka nan, majiyoyi sun ce an sauya tafiyar shugaban kasa Tinubu daga Abuja zuwa Lagos a lokuta daban-daban saboda bayanan tsaro, lamarin da ya hada da soke bikin 1 ga Oktoba.
Duk da musun rundunar soji cewa akwai yunkurin juyin mulki, bayanan sirri na ci gaba da nuna akasin haka, inda aka ci gaba da kama wasu hafsoshi da binciken manyan mutane ciki har da tsohon gwamna Timipre Sylva.
Rahotanni sun kuma ce mafi yawan wadanda aka kama daga Arewa ne, abin da ya sa hukumomi ke taka-tsantsan wajen bayyana sunaye domin kaucewa rikicin siyasa da kabilanci a rundunar.
Juyin mulki: Sojoji 2 sun tsere zuwa ketare
Kun ji cewa Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami’ai biyu sun tsere bayan sun shiga cikin jerin wadanda ake zargi da shirin juyin mulki.
Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an da suka tsere sun hada da wani Manjo daga jihar Taraba da kuma daya daga birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
EFCC ta kaddamar da binciken wadanda ake zargi da shirya kifar da Gwamnatin Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa sama da jami’an soja 30 yanzu suna tsare da ake bincike kan zargin juyin mulki wanda ya ta da hankula a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
