Shugabannin Kasashen da Suka Fi Kowa Dadewa a Mulki a Yau a Afrika

Shugabannin Kasashen da Suka Fi Kowa Dadewa a Mulki a Yau a Afrika

A halin yanzu, nahiyar Afrika na da wasu shugabanni da suka shafe tsawon shekaru suna mulki kuma suka haura shekaru 70 da haihuwa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika sun haura shekaru30 a mulki
Yoweri Kaguta Musaveni na Uganda, Paul Biya na Kamaru da Theodore Obiang Nguema na Equatorial Guinea Hoto: Yoweri Kaguta Musaveni/Kebane/Luis Tato
Source: Facebook

Ƙasashen Africa – Wasu daga cikinsu sun dade a karagar mulki fiye da shekaru 30, kuma har yanzu suna fafutukar cigaba da zama a karagar mulkin kasashensu.

Legit ta tattaro maku wasu daga cikin wadannan shugabanni ta cikin wannan rahoto:

1. Paul Biya na Kamaru

Paul Biya shi ne shugaban kasa mafi tsufa da ke rike da mulki a nahiyar Afrika a halin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya karɓi ragamar mulki tun daga shekarar 1982, wanda hakan ke nufin ya shafe sama da shekaru 40 yana jan ragamar kasar Kamaru.

Paul Biya ya sake lashe zabe a Kamaru
Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya Hoto: Kebane
Source: Facebook

BBC ta wallafa cewa duk da yawan shekaru da yake da su – yanzu yana da shekara 92 – Biya har yanzu yana ci gaba da shugabanci bayan hukumomin kasar sun tabbatar da zabensa a watan Oktoban 2025

Kara karanta wannan

Trump ya sa Najeriya a jan layi kan zargin kashe Kiristoci, Amurka za ta yi bincike

A lokuta da dama, ‘yan kasar da kungiyoyi na duniya sun yi kira da ya mika mulki, amma har yanzu bai nuna wata alama ta yin hakan ba.

2. Alassane Ouattara na Ivory Coast

Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara, yana daya daga cikin tsofaffin shugabannin Afrika da suka haura shekaru 80.

TVC News ta wallafa cewa ya karɓi mulki tun daga 2011 bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan zaben shugaban kasa, yanzu ya doshi shekaru kusan 15 a karagar mulki.

Tun daga lokacin, ya tabbatar da kafa tsarin tattalin arziki mai karfi a kasar, musamman a bangaren noma da kasuwanci.

3. Yoweri Museveni na Uganda

Yoweri Kaguta Museveni ya shafe sama da shekaru 38 a karagar mulki, bayan ya karɓe iko daga sojoji a 1986.

Museveni ya kasance daya daga cikin manyan shugabannin Afrika da suka dade suna mulki fiye da kowane shugaba a yankin Gabashin Afrika.

Yoweri Kaguta Musaveni na cigaba da mulkin Uganda
Yoweri Kaguta Musaveni, Shugaban kasar Uganda Hoto: Yoweri Kaguta Musaveni
Source: Facebook

The Independent ta wallafa cewa yanzu haka Shugaba Yoweri Museveni ya fara gangamin neman zabe a yankin Teso domin ci gaba da mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta kare sanya harajin 15% da zai jawo tashin farashin fetur

Duk da matsin lamba daga ‘yan adawa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, Museveni ya ci gaba da lashe zabe, yana mai cewa shi ne “garkuwar zaman lafiya da ci gaban Uganda.”

4. Theodore Obiang Nguema na Equatorial Guinea

Theodore Obiang Nguema shi ne shugaban da ya fi dadewa a mulki a duk duniya, ba a Afrika kadai ba.

Theodore Obiang Nguema na daga cikin shugabanni da suka dade a mulki
Theodore Obiang Nguema, shugaban kasar Equatorial Guinea Hoto: Luis Tato
Source: Getty Images

Ya hau mulki tun daga shekarar 1979 bayan juyin mulki da ya kifar da shugaban kasa na wancan lokaci, wanda kuma kawunsa ne.

The Nation ta ruwaito cewa a yau, Nguema ya shafe fiye da shekaru 45 yana mulki, kuma ya ci gaba da rike da ragamar kasarsa.

Duk da samun arzikin man fetur a kasar, ana yawan suka ga gwamnatin sa saboda rashin dimokuradiyya da yancin ‘yan kasa.

5. Isaias Afwerki na Eritrea

Isaias Afwerki shi ne shugaban farko kuma na yanzu da Eritrea ta taɓa samu tun bayan samun ‘yancin kanta daga Habasha a watan Mayun 1993.

Ya shafe sama da shekaru 29 yana mulki, inda ake kallonsa a matsayin shugaba mai karfin iko da tsaurin ra’ayi a yankin 'Horn of Africa.'

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki

Isaias Afwerki ne Shugaban Eritrea tun bayan da kasar ta samu yanci
Hoton Shugaban kasar Eritrea, Isaias Afwerki Hoto: Great Africa
Source: Facebook

VOA ta wallafa cewa Afwerki ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin neman ‘yancin kai na Eritrea, wanda ya kare da nasarar da ta kawo cikakken ‘yanci ga kasar.

Ana zargin bayan samun mulki, ya kafa tsarin mulki mai cike da takunkumi, inda babu ‘yancin kafafen yada labarai, jam’iyyun siyasa, ko zaben da ke ba ‘yan kasa damar fitar da ra’ayinsu.

A yau, Isaias Afwerki na daga cikin tsofaffin shugabanni da suka fi dadewa a mulki a Afrika, kuma ya ci gaba da kasancewa ginshiƙi a siyasar kasa.

Ana kalubalantar Shugaba Paul Biya

A baya, mun wallafa cewa Issa Tchiroma Bakary, ɗan adawa daga ƙasar Kamaru, ya fitar da jawabi inda ya ce ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar kwanakin baya.

Ya bayyana cewa “jama’a sun zaɓe shi” a zaɓen da aka fafata, kuma ya jawo hankalin Shugaba Paul Biya da ya taya shi murna bisa wannan nasara da ya ce samu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Sai dai, gwamnatin Kamaru ta yi gargaɗi cewa ba kowa ne ke da hurumin ayyana wanda ya lashe zabe ba, illa hukumar tsarin mulki, saboda haka ya ja kunnen Bakary.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng