Amfanin da Mazauna Sababbin Jihohi da Za a Iya Kirkira Za Su Samu a Najeriya
- Ana ta ci gaba da fadar ra'ayoyi game da shirin kirkirar sababbin jihohi a Najeriya domin kara yawansu daga 36 da ake da su yanzu
- Masana sun ce kirkiro sababbin jihohi a Najeriya na kara wa yankuna da kabilun da aka dakile damar samun karfi da wakilci a siyasa
- Hakan ya biyo bayan kokarin da majalisar tarayya ke yi domin samar da sababbin jihohin daga yankuna daban-daban
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kirkirar sababbin jihohi a Najeriya ta sake tayar da mahawara kan tasirin hakan ga al'umma da kuma shugabanci da ci gaban kasa
Masana da yan gwagwarmaya sun ce wannan tsari zai kawo fa’ida ga jama’a, daga karin wakilci har zuwa farfado da tattalin arziki.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya ce kwamitin majalisar tarayyya ya amince da kirkirar sababbin jihohi shida a yankunan da ake da su a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yanzu haka, yankin Kudu maso Gabashin kasar shi ne ke da mafi karancin jihohi guda biyar yayin da sauran ke da shida har sama.
Yankin Arewa maso Yamma ne kadai ke da jihohi har guda bakwai a kasar yayin da sauran ke da shida bayan Kudu maso Gabas da ke da biyar kacal.
A yan kwanakin nan, majalisar tarayya na ci gaba da tattaunawa domin samar da sababbin jihohin a Najeriya daga guda 36 da ake da su.
Sababbin jihohi: Moriyar da mutane za su samu
Legit Hausa ta yi bincike kan amfanin da mazauna sababbin jihohin da za a kirkira za su samu idan aka tabbatar da su a kasar:
1. Karin wakilci da shigar da al’umma siyasa
Masana sun ce sabuwar jiha kan ba yankuna da kabilun da aka dade ana dannewa damar samun karfi a siyasa.
Saboda suna kafa tsarin mulkinsu, hakan na basu karin kujeru a majalisa da mukamai a gwamnati.

Kara karanta wannan
Jiha 1 ta fita daban, jihohi 35 sun dogara da gwamnatin tarayya duk da samun N17trn
Masana siyasa sun kara cewa hakan na rage rinjayar manyan kabilu, tare da karfafa tattaunawa tsakanin kowa da kowa a Najeriya.
2. Gaggawar ci gaban kasa daga tushe
Kwarraru sun bayyana cewa samar da sababbin jihohi kan kawo gwamnati kusa da jama’a wanda ke kara ci gaba.
Sababbin biranen gwamnati kan samu damar gina tituna, asibitoci, makarantu, wutar lantarki da ayyukan more rayuwa.
Jama’a kan fi samun kulawar gwamnati da rarraba albarkatu cikin adalci idan har aka samar da sabuwar jiha.

Source: Facebook
3. Karfafa tattalin arziki da amfani da albarkatu
Masana tattalin arziki sun ce sababbin jihohi kan baiwa yankuna ikon bunkasa arzikin yankinsu, cewar rahtoton Nigeria First Vanguard.
Hakan na baiwa jihohi damar tsara manufofin noma, masana’antu da yawon bude ido bisa karfin yankinsu.
Wannan yana kara samar da ayyukan yi ta hanyar gina ofisoshin gwamnati, ayyuka ga kamfanoni da karin zuba jari.
4. Haɗin kan kasa da kwanciyar hankali
Masu nazarin tsaro sun ce baiwa yankuna jihar kansu na rage bore, tashin hankali da rikice-rikice.
Yankuna kan samu jin dadin kasancewa cikin kasa, saboda ana ganin an basu matsayi da za a rika damawa da su.
Hakan na inganta zaman lafiya da hadin kai tsakanin kabilu da yankuna daban-daban saboda ba su dama da aka yi.

Source: Getty Images
5. Karfafa tsarin tarayya da dimokuraɗiyya
Masana doka sun ce kirkiro sababbin jihohi na karfafa tsarin tarayya, domin yana ba jihohi ikon gudanar da manufofi bisa bukatunsu.
Hakan na haifar da gasa mai kyau tsakanin jihohi wajen kawo ci gaba da ingantaccen shugabanci.
A cewar masana, wannan tsarin na karfafa ci gaban siyasa da tattalin arziki a matsayinta na kasa mai tsarin dimokuraɗiyya.
A karshe, Premium Times ta ce masana sun ce sababbin jihohi na taka muhimmiyar rawa wajen inganta dimokuraɗiyya, ci gaba, da shigar kowa cikin tsarin mulki.
Majalisa ta amince a kirkiri jihohi 6
A wani labarin mai kama wannan, kun ji cewa akwai yiwuwar jihohin da ake a Najeriya su kara daga guda 36 zuwa 42 bayan an amince da kirkiro sababbi.
Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai ya amince da kirkiro karin jihohi guda shida a yankuna da ake da su a Najeriya.
Amincewar na zuwa ne bayan kwamitin ya duba bukatu 55 masu neman a kirkiro karin jihohi a Najeriya wanda ya jawo ra'ayoyi mabambanta a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


