APC Ta Samu Rinjaye, Ta Kulle Damar Tsige Shugaban Ƙasa a Majalisa

APC Ta Samu Rinjaye, Ta Kulle Damar Tsige Shugaban Ƙasa a Majalisa

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta samu rinjayen kashi biyu bisa uku a Majalisar Wakilai, bayan karin wasu ‘yan majalisa guda shida da suka sauya sheƙa
  • Tsofaffin 'yan majalisar PDP da LP ne suka baiwa APC sabon matsayin, inda a yanzu tana da kujeru 243 daga cikin kujeru 360, yayin da PDP ta ragu zuwa 72
  • Masana sun yi gargadi cewa wannan rinjaye na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya idan babu isassun hanyoyin duba daidaito a cikin majalisar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja– Jam’iyya mai mulki ta APC ta ƙara samun ƙarfi a Majalisar Wakilai bayan wasu ‘yan majalisa guda shida daga jam’iyyun adawa suka sanar da sauya sheƙa.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar akwai ‘yan PDP biyar daga Jihar Enugu – Nnolim John Nnaji, Anayo Onwuegbu, Oke Martins.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: 'Yan majalisar PDP 5 a Enugu sun koma jam'iyyar APC

APC ta mamaye majalisun Najeriya
Hoton Shugaban kasa, Bola Tinubu a gaban 'yan majalisa Hoto: @PBAT
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sauran sun hada da Obetta Mark Chidiebere, da Dennis Nnamdi Agbo, sai kuma kuma Daniel Asama daga Filato, wanda ya bar LP zuwa APC.

APC ta kara karfi a majalisar tarayya

Trust Radio ta ruwaito cewa da yake magana a madadin ‘yan Enugu, Hon. Nnolim Nnaji ya ce matakin nasu “yunkuri ne na haɗa kai da gwamna Peter Ndubuisi Mbah” domin ci gaban jihar.

Ya ce:

“Mun yanke shawarar wannan sauyi da nufin kawo sabon salo a siyasar Enugu da Najeriya gaba ɗaya.”
APC ta samu rinjayue a majalisar wakilai
Hoton Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen Hoto: Tajudeen Abbas
Source: Facebook

A yanzu, APC na da kujeru 243 a majalisar da ke da 'yan majalisa 360, yayin da PDP ke da 72, LP 21, NNPP 15, APGA 5, SDP 2, ADC 1, da YPP 1.

Wannan ya bai wa APC rinjayen da zai ba ta damar tabbatar da bukatar gwamnati a muhimman batutuwan dokoki da gyaran kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

APC ta jero sunayen gwamnan Filato da gwamnoni 3 da za su sauya sheka kafin karshen 2025

Tasirin rinjayen APC ga dimokuraɗiyya

Masana sun bayyana cewa samun rinjayen kaso biyu bisa uku a majalisun biyu na ƙasa yana da tasiri sosai ga tsarin doka da siyasa a ƙasar.

Bisa tsarin mulkin 1999, duk wani gyaran kundin tsarin mulki dole ne ya samu amincewar kashi biyu bisa uku na kowace majalisa.

Wannan yana nufin APC na iya tura kudirin gyara kundin tsarin mulki cikin sauƙi — duk da cewa amincewar majalisun jihohi har yanzu tana da muhimmanci.

Haka kuma, wannan rinjaye yana bai wa APC damar kare shugaban ƙasa daga yiwuwar kaddamar da muhawarar tsige shi.

Sai dai, Farfesa Gbade Ojo, masani kan siyasa, ya yi gargadin cewa irin wannan rinjaye na iya raunana dimokuraɗiyya.

Ya ce:

“Idan jam’iyya ɗaya ta mamaye majalisa gaba ɗaya, za a rasa daidaito da ikon duba ayyukan juna. Wannan hatsari ne ga demokuraɗiyyar mu.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyun adawa sun gaza ƙarfafa kansu, abin da ya sa suka rasa tasiri a siyasar ƙasa.

Kara karanta wannan

"Laima ta yage,' Sanata Agadaga ya kara ruguza PDP, ya sauya sheka zuwa APC

Majalisa ta amince da kirkirar jihohi 6

A baya, kun ji cewa kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan sake duba kundin tsarin mulki ya amince da kirkiro karin jihohi guda shida a kasar nan.

'Yan majalisa sun cimma wanan matsaya ne a taron bita na kwanaki biyu da aka gudanar a Legas karkashin jagorancin Sanata Barau I. Jibrin da Rt. Hon. Benjamin Kalu.

A yayin taron, kwamitin na hadin gwiwa ya tattauna kan kudirori 69, bukatu 55 na kirkirar jihohi, bukatu 2 na gyaran iyaka, da bukatu 278 na kirkirar kananan hukumomi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng