Juyin Mulki: An Kara Samun Bayanan Sojojin da Ake Zargin Sun Shirya Kifar da Tinubu
- An kara samun bayanai kan sojoji 16 da ake zargin su na tsare kan jita-jitar shirin juyin mulki a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kunshi jami'an rundunar sojojin kasa 14 da jami'i daya daga rundunar sojojin ruwa da sojan sama daya
- Hedktwatar tsaro dai ta musanta batun juyin mulkin da ake ta yadawa, inda ta ce ta tsare sojojin ne kan wasu dalilai daban
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya - Wasu bayanai sun kara fitowa kan dakarun rundunar sojojin Najeriya 16 da ake tsare da su kan zargin hannu a shirin yi wa Shugaba Bola Tinubu juyin mulki.
Bisa ga majiyoyi masu kusanci da lamarin, daga cikin jami’an 16 da ake tsare da su, 14 sojojin ƙasa ne, sai kuma sojan ruwa daya da kuma sojan sama daya.

Source: Facebook
Bayanan sojoji 16 da ake zargi da hannu
Premium Times ta tattaro cewa sojojin kasa da ake zargi sun hada da Birgediya Janar ɗaya, Kanal ɗaya, Laftanar Kanal huɗu, Manjo-Manjo guda biyar, Kaftin biyu da Laftanar ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na Rundunar Ruwa kuma Lieutenant Commander ne (daidai da Manjo a Rundunar Sojojin Ƙasa), sai kuma sojan sama da ya kai matsayin Squadron Leader ne (daidai da Manjo).
Majiyoyi sun bayyana cewa daga cikin sojojin ƙasa 14, 12 daga cikin su ’yan Infantry Corps ne, watau sashen da ke gudanar da yaƙi kai tsaye a filin fama.
Sai kuma daya na sashen da ke kula da sadarwa, yayin da wani kuma daga Ordnance Corps, wanda ke da alhakin killace makamai da kula da su.
Rahotanni sun nuna cewa mafi yawansu ’yan rukuni na 56 ne da aka yaye daga makaran sojoji ta NDA, waɗanda suka yi horo daga 27 ga Satumba 2004 zuwa 4 ga Oktoba 2008.

Kara karanta wannan
Mintuna 30 a tsakani, jirage sama 2 na rundunar sojoji sun yi hatsari, sun fada teku
Daga wadanne yankuna sojojin suka fito?
Majiyoyi sun kuma tabbatar da cewa 15 daga cikin sojojin da ake tsare da su sun fito ne daga yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Sai ɗaya tilo daga cikin su, wani da ya kai matsayin Lafatanar wanda ya fito daga yankin Kudu maso Yamma.
Tuni dai rundunar sojojin Najeriya ta fara bincike kan wani yunkuri da ake zargin na juyin mulki ne wanda bai kai ga nasara ba a ƙarshen watan Satumba.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce majiyoyi masu tushe sun shaida mata cewa masu yunkurin juyin mulkin sun shirya kashe manyan jami’an gwamnati ciki har da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima.
Sai dai rundunar sojojin ba ta tabbatar da zargin juyin mulkin kai tsaye ba, inda ta bayyana cewa binciken da ake yi “na cikin gida ne, domin tabbatar da ɗa’a da ƙwarewa a cikin rundunar.”

Kara karanta wannan
Dalilin Buhari da Tinubu na korar Janar 500 daga rundunar tsaro duk da matsalar ta'addanci
Sylva na da hannu a shirin juyin mulki?
A wani labarin, mun kawo maku cewa tsohon Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva ya musanta hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Mai magana da yawun tsohon ministan, Cif Julius Bokoru, ya karyata jita-jitar da ke cewa Sylva na da hannu a wani yunƙurin juyin mulki.
Bokoru ya zargi wasu ‘yan siyasa da ke kwadayin mulki a 2027 da yada jita-jitar juyin mulki saboda su na ganin Sylva a matsayin babban cikas ga burinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
