'Za Su Rika Gudu,' Sabon Shugaban Sojan Sama Ya Fadi yadda zai Birkita 'Yan Ta'adda

'Za Su Rika Gudu,' Sabon Shugaban Sojan Sama Ya Fadi yadda zai Birkita 'Yan Ta'adda

  • Sabon shugaban rundunar sojin sama, Sunday Kelvin Aneke, ya ce zai gina runduna mai saurin kai hari wacce za ta hana ‘yan ta’adda sakat
  • Ya bayyana cewa rundunar za ta kasance mai ƙwarewa, fasaha, da kuma tsari na kimiyya wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan
  • An tabbatar da nadin sa ne bayan amincewar majalisar dattawa a ranar 29, Oktoba, 2025, bisa izinin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Sabon shugaban rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF), Sunday Kelvin Aneke, ya yi alkawarin jagorantar runduna mai fasaha, ladabi, da kwarewa.

Ya bayyana cewa rundunar da zai jagoranta za ta hana ‘yan ta’adda damar samun lokacin shirya kai hare-hare.

Sunday Kelvin Aneke
Shugaban sojan sama, Sunday Aneke a majalisa. Hoto: Nigeria Air Force
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da sabon shugaban ya yi ne a wani sako da rundunar sojan saman ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Ana neman CBN ya kawo sababbin takardun kudin N10,000 da N20,000 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa manufarsa ita ce gina rundunar da za ta rika amsa kiran gaggawa a kan lokaci tare da kai hari daidai da ka’ida.

Manufofin shugaban sojojin sama

A yayin bayani ga majalisar dattawa, Sunday Aneke ya ce manufarsa ta shugabanci ta ta’allaka ne kan horo, fasahar zamani, tsaro, da kirkire-kirkire a harkokin dabarun soji.

Yayin da ya ke karin haske kan yadda zai firgita 'yan ta'adda su fara gudu, su gagara zama, ya ce:

“Wanda yake gudu daga gare ka ba zai samu damar shirya kai hari ba,”

Ya kara da cewa rundunar da yake jagoranta za ta kasance mai amsa kira cikin gaggawa, kai hari daidai, da kuma yin aiki cikin hikima a dukkan fannoni na ayyukan soja.

Tarihin aiki da amincewa da Sunday Aneke

Daraktan yada labarai na rundunar, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa tabbatar da nadin Aneke ya biyo bayan amincewar shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa doka.

Kara karanta wannan

Shirin juyin mulki: Sojoji sun bi diddigin N45bn zuwa hukumar raya Neja Delta

Da wannan tabbaci, ya maye gurbin Hasan Bala Abubakar, kuma ya zama ɗaya daga cikin mambobin majalisar sojojin Najeriya.

Vanguard ta wallafa cewa Aneke ya taba zama kwamanda a bangaren zirga-zirga, inda ya inganta dabarun jigilar sojoji da karfafa hadin kai tsakanin sassan tsaro.

Haka kuma, ya taka muhimmiyar rawa a fannin leken asiri da sa ido, wanda ya taimaka wajen nasarar yaƙin da Najeriya ke yi da ‘yan ta’adda da masu tada hankali.

Majalisar kasa ta amince da Sunday Aneke

’Yan majalisa sun yaba da zurfin ilimi da gogewar Sunday Aneke a fannoni daban-daban na dabarun soji.

Sunday Kelvin Aneke
Shugaban sojojin saman Najeria yayin tantance shi a majalisa. Hoto: Nigeria Air Force
Source: Facebook

Sun ce kwarewarsa a harkokin tsaro da horarwa ta nuna cewa yana da hangen nesa na sauya fasalin rundunar.

Taron tabbatar da nadinsa ya samu halartar ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisa, Sanata Basheer Lado.

'Yan bindiga sun saka haraji a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sanya harajin N15m kan wasu mutane a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Mintuna 30 a tsakani, jirage sama 2 na rundunar sojoji sun yi hatsari, sun fada teku

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa a yankin Bazar na karamar hukumar Yabo aka sanya harajin.

Mutanen Bazar sun yi kira ga gwamna Ahmed Aliyu Sokoto da ya taimaka ya dauki matakin gaggawa kan lamarin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng