Ba Yan Ta'adda ba ne: Yan Sandan Jigawa Sun Wanke Mutanen da Suka Shigo da Makamai

Ba Yan Ta'adda ba ne: Yan Sandan Jigawa Sun Wanke Mutanen da Suka Shigo da Makamai

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi magana a kan sahihancin wani bidiyo da ke nuna gungun mutane da ake zargin 'yan taadda
  • A bidiyon, an rika yada cewa gungun yan ta'adda sun shiga Jigawa ne daga wasu sassan kasar nan yayin da ake fama da matsalar tsaro a kasa
  • Tuni rundunar ta yi martani, inda ta shaidawa jama'a cewa su kwantar da hankulansu, tare da yin watsi da bidiyon da abin da ya kunsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa – Hedikwatar rundunar 'yan sandan Jigawa tafito da bayanai bayan wani bidiyo da ke nuna taron mutane da aka ce 'yan ta'adda ne ke shiga jihar.

A sanarwar da kakakin rundunar, SP Shiisu Adam ya fitar ga manema labarai, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a labarin da ke cewa 'yan ta'adda sun shiga Jigawa.

Kara karanta wannan

APC ta tanka da Gwamna Mutfwang ya ce ana matsa masa lamba ya koma jam'iyyar

Yan sanda sun yi bayani game da mutanen da suka shiga Jigawa da makamai
Hoton Sufeton yan sandan kasa, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

TVC News ta wallafa cewa sanarwar ta ce ana yada labarin karyar ne domin a jefa jama'a a cikin tashin hankali da zaman dar-dar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sandan Jigawa sun yi magana kan batun

SP Shiisu Lawan Abdullahi ya shaidawa majiyar Legit cewa 'yan sanda sun gudanar da cikakken bincike a kan bidiyon da ikirarin da ake yi na cewa 'yan ta'adda ne suka sauka a Jigawa.

Ya kara da cewa mutanen da aka gani a bidiyon ba ‘yan ta’adda ba ne, mafarauta ne na kungiyar “Peace and Security Service Organisation” daga jihar Bauchi.

Yan sandan Jigawa sin ce suna aiki tukuru don wanzar da zaman lafiya
Hoton wasu jami'an yan sanda a bakin aiki Hoto: Nigeria Police Force
Source: Getty Images

SP Shiisu Abdullahi ya kara da cewa mafarautan na dawowa daga wani taro da suka halarta a garin Chai-Chai Sabuwa da ke karamar hukumar Ringim.

Rundunar ta bayyana cewa mutanen suna cikin kayan aikinsu na gargajiya, dauke da bindigu irin na gargajiya, baka da kibau, wanda ya sa wasu suka yi tunanin ‘yan bindiga ne.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP a Borno, an tura tsageru zuwa barzahu

'Yan sandan Jigawa sun roki jama'a

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Jigawa, Dahiru Muhammad, ya roki jama’a da su yi watsi da bidiyon gaba ɗaya, tare da kwantar da hankalinsu su ci gaba da bin doka da oda.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kara da cewa jama’a su ci gaba da bayar da rahoto kan duk wani motsi ko mutum da suke zargi, domin taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da aikinsu.

Ya kara da cewa:

“Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ko’ina cikin jihar."

Rundunar ta kuma bukaci masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji yada bayanan karya ko wadanda ba a tabbatar da gaskiyarsu ba.

'Yan sandan Jigawa sun cafke barawon mota

Kara karanta wannan

Kungiyar Amnesty Int'l ta yi magana da Hisbah ta kama masu shirin 'auren jinsi' a Kano

A baya, mun wallafa cewa jami’an hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) reshen Jigawa sun samu nasarar kamo wani matashi a bisa zargin satar wata mota ta asibiti daga ƙasar Nijar.

Shugaban NIS na jihar Jigawa, Tahir Abdullahi Musa, ya tabbatar da cewa an kama matashin da ake zargi mai suna Yusif Bashir, yayin da ya ke shirin shigowa da motar ta Babura.

Ya ce matashin ya sato motar asibiti, wacce ma’aikatan lafiya ko asibiti ke amfani da ita – amma aka sace ta kuma an shigo da ita ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya ja hankalin jami'ansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng