Mutanen Birnin Tarayya za Su Zauna a Duhu, TCN Ya Fadi Dalilin Dauke Wuta a Abuja
- Kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da cewa za a samu rashin wuta na wucin gadi a wasu yankunan babban birnin tarayya, Abuja
- Sanarar kamfanin ta ce rashin wutar zai shafi layin wutar Gwagwalada–Kukwaba–Apo daga 28 ga Oktoba zuwa 16 ga Nuwamba 2025.
- TCN ya nemi jama’a da su yi hakuri, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaron ma’aikata da aikin da za a gudanar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa, TCN ya bayyana cewa wasu yankuna a babban birnin tarayya, Abuja, za su fuskanci katsewar wutar lantarki.
Kamfanin ya bayyana cewa amma wannan matsala ba za ta dauki lokaci mai tsawo ba, inda ya ce daukar matakin katse masu wuta ya zama dole.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa za a samu matsala ne sakamakon aikin gina hanya da ke gudana a yankin Kuje da hukumar raya birnin Abuja (FCDA) ke yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TCN ya ce za a yi rashin wuta
This day ta wallafa cewa TCN ya bayyana cewa aikin zai gudana ne daga ranakun Talata, 28 ga Oktoba, zuwa Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025.
Sanarawar kamfanin ta ce:
“Aikin zai shafi layin wutar 132kV Gwagwalada–Kukwaba–Apo Double Circuit Transmission Line."
“A saboda haka, TCN za ta gudanar da aikin daidaita lodin wuta domin kaucewa hadurra da kare ma’aikata da dukkannin masu ruwa da tsaki a aikin.”
Kamfanin ya kara da cewa rashin wutar zai kasance a matakai uku domin rage cikas ga jama’a da bai wa aikin damar tafiya yadda ya kamata.
TCN ya yi bayani kan dauke wuta
TCN ya bayyana cewa mataki na farko zai fara daga ranar 28 ga Oktoba zuwa 2 ga Nuwamba 2025, daga 9.00 na safe zuwa 5.00 na yamma kowace rana.

Kara karanta wannan
Sule Lamido ya fara daukar matakin shari'a, ya kai PDP kotu kan hana shi neman takara

Source: Facebook
Mataki na biyu kuma zai gudana daga 6 zuwa 9 ga Nuwamba, 2025 yayin da mataki na uku zai kasance daga 12 zuwa 16 ga Nuwamba 2025, tsakanin 9.00 na safe zuwa 3.00 na rana.
Yankunan da za su fi fuskantar wannan matsala sun haɗa da Apo, Lokogoma, Guzape, Asokoro, Wuye, Utako, Jabi, da Idu Industrial Layout.
TCN ya tabbatar da cewa wutar za ta koma yadda take a ƙarshen kowace rana bayan ma’aikata sun kammala aikin gina hanya.
Kamfanin ya baiwa jama'a hakuri,yana mai cewa wannan ba a dauki matakin domin cutar da su ba, sai domin samar da cigaba a Abuja.
Tinubu ya ba jihohi ragamar wutar lantarki
A baya, kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fitar da doka da ke baiwa jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu damar shiga harkar samar da wutar lantarki da rarraba ta.
Wata dokar 2023 ta bayyana cewa jihohi za su iya ba da lasisi ga wadanda za su samar da wuta kuma su rarraba ta a matakin jiha, ba sai sun dogara kacokan ga gwamnatin tarayya ba.
Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka domin rage matsalar ƙarancin wuta da ake fama da ita a jihohi musamman a shiyyoyin Arewa da yankuna karkara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

