Gwamna Bago Ya ba da Hutun Kwanaki 2, Ya Umarci Jama'a Su Takaita Zirga Zirga
- Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago ya ba da hutun kwanaki saboda zaben kananan hukumomin da za a yi ranar Asabar mai zuwa
- Sakataren gwamnatin Neja, Abubakar Usman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025
- Ya ce gwamnatin jihar Neja ta ba da umarnin takaita zirga-zirgan ababen hawa, sai wanda aikinsa ya zama dole kuma yake da izini
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Minna, Jihar Neja – Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar hutun kwanaki biyu saboda zabe.

Kara karanta wannan
"Borno ta APC ce," Gwamna Zulum ya tuna alherin da Buhari da Tinubu suka kawo a Arewa
Gwamna Bago ya ayyana Alhamis 30 ga Oktoba da Juma’a 31 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranakun hutu na aiki a fadin jihar Neja.

Source: Twitter
Me yasa Gwamna Bago ya bada hutu?
Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa Gwamna Bago ya ba da hutun ne domin bai wa jama’a damar halartar zaben kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Abubakar Usman, ya fitar a Minna, babban birnin Neja yau Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025.
Ya ce gwammatin Neja ta dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa kowane dan kasa ya samu damar zuwa mazabarsa ya kada kuri'a kamar yadda doka tanada.
Sanarwar ta bayyana cewa kasuwanni, bankuna, cibiyoyin kudi da ofisoshin gwamnati za su kasance a rufe a wadannan kwanakin hutu guda biyu.
Gwamma Bago ya sa dokar hana zirga-zirga
Abubakar Usman ya kara da cewa gwamnati ta sanya dokar takaita zirga-zirgar mutane da motoci, sai dai waɗanda ke kan ayyukan gaggawa ko masu izini na musamman.
“Gwamnati na kira ga al’ummar Jihar Neja da su fito kwansu da kwarkwatarsu su yi amfani da wannan dama wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu, ta hanyar kada kuri’a a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025,” in ji Abubakar.
Ya ƙara da cewa wannan zabe yana da muhimmanci wajen bai wa jama’a damar zaɓar shugabannin da za su wakilce su a matakin ƙananan hukumomi.
A cewarsa, shugabannin kanananan hukumomi su ne suka fi kusa da jama'a, wadanda za su kawo ci gaban da zai taimaki rayuwar al'umma, cewar jaridar Punch.

Source: Facebook
Gwamna Bago ya hada kai da jami'an tsaro
A cewar Sakataren, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su tabbatar an gudanar da zaben cikin natsuwa, zaman lafiya da gaskiya.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas wajen aiwatar da sahihi kuma ingantaccen zabe ba.
An kama dalibin da ya soki Gwamna Bago
A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun kama wani dalibin jami'a, Abubakar Isah Mokwa bisa zargin sukar Gwamma Mohammed Umaru Bago a jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa ɗalibin ya wallafa wasu kalamai na sukar ayyukan Gwamna Bago a Facebook, wanda hakan ya kai ga kunnen gwamnatin Neja.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa an kama shi ne a masaukinsa da ke wajen harabar jami’a a Lapai ranar Alhamis da daddare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

