Karfafa Noma: Majalisa na Son a Daina Shigo da Shinkafa Sosai daga Ketare

Karfafa Noma: Majalisa na Son a Daina Shigo da Shinkafa Sosai daga Ketare

  • Ana fara daukar matakan rage dala biliyan biyu da ake kashewa wajen shigo da shinkafa ta hanyar kafa hukuma ta musamman
  • Majalisar dattawa ta gabatar da kudirin ne domin karfafa bincike da tallafa wa manoma domin inganta harkar shinkafa a fadin kasar nan
  • An ce kudirin na daga cikin manufofin gwamnatin Bola Tinubu na “Renewed Hope” don karfafa tattalin arziki da wadatar abinci a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar dattawan Najeriya ta fara shirin kafa hukuma ta musamman kan samar da shinkafa a Najeriya.

Za a kafa hukumar ne domin rage dogaro da shigo da shinkafa daga kasashen waje da kuma karfafa samar da ita a cikin gida.

Majalisar dattawan Najeriya
Zauren majalisar dattawan Najeriya. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Rahoton The Cable ya nuna cewa Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya ne ya gabatar da kudirin a majalisa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce an yi abin kunya a filin wasan Kebbi da aka gina da kudin FIFA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudirin na da nufin bunkasa bincike, inganta dabarun noma, da karfafa masana’antun sarrafa shinkafa a fadin kasar.

A cewar majalisar, kafa hukumar zai zama muhimmin mataki wajen cimma burin gwamnati na tabbatar da wadatar abinci da samar da ayyukan yi ga matasa da mata.

Rage shigo da shinkafa zai karfafa noma

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wanda Mohammed Monguno ya wakilta, ya bayyana cewa mataki na cikin shirin “Renewed Hope” na shugaban kasa Bola Tinubu.

The Nation ta rahoto ya ce:

“Kudirin kafa hukumar harkokin shinkafa a Najeriya zai taimaka a rage kashe kudi wajen shigo da shinkafa, samar da ayyuka da kuma mayar da Najeriya cibiyar samar da shinkafa a nahiyar Afirka.”

Amfanin hukumar shinkafa a Najeriya

Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin noma, Sanata Salihu Mustapha, ya ce shinkafa abinci ce da ta zama jigo a kusan kowane gida a Najeriya.

Sai dai duk da haka ya ce masu casar shinkafa na fama da matsaloli duk da damar da ake da ita ta samar da ton miliyan bakwai a shekara.

Kara karanta wannan

Sauya kundin mulki: Majalisa ta fara bitar bukatun kirkirar jihohi 55 a Najeriya

gonar shinkafa a Najeriya
Yadda aka noma shinkafa a wata gona. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce kudirin zai tabbatar da kafa hukumar da za ta mayar da hankali kan bincike, horaswa, da kirkirar sababbin hanyoyi da iri masu jure ambaliya zuwa injunan sarrafa shinkafa na zamani.

Mustapha ya kara da cewa mataki zai rage dogaro da shigo da shinkafa da darajar ta kai Dala biliyan 2, tare da kafa masana’antu a Arewa da Kudu, da kuma habaka manoma.

Martanin masu casar shinkafa a Najeriya

Kungiyar masu casar shinkafa ta RIMAN ta bayyana goyon bayanta ga wannan kudiri, tana mai cewa lokaci ne da ya dace domin bude kofa ga cigaban samar da shinkafa a kasar.

Shugaban kungiyar, Peter Dama, ya lissafo kalubalen da suke fama da su kamar rashin tsaro, rashin isasshen ruwa, da rashin kayan aiki na zamani.

ADC ta yi magana kan farashin abinci

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi martani kan saukar farashin kayan da aka noma a Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar mata su karu a majalisa, gwamnoni sun goyi bayan kudiri na musamman

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ikirarin gwamnatin tarayya na cewa yawan noma ne ya karya abinci ba gaskiya ba ne.

Ya ce abu ne sananne rashin tsaro ya hana manoma da dama zuwa gona baya ga tsadar taki da sauran kayan noma a damunar bana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng