Gwamna Mutfwang Ya Fadi Matsayarsa bayan Fuskantar Matsin Lambar Ya Koma APC
- Gwamnan jihar Plateau ya yi tsokaci kan batun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya
- Caleb Mutfwang ya bada tabbacin cewa wasu manyan 'yan siyasa sun matsa masa lamba kan ya koma jam'iyyar APC
- Sai dai, gwamnan ya nuna abubuwan da za su iya sanyawa ya bar PDP wadda ya lashe zabe karkashinta a shekarar 2023
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana matsin lambar da yake fuskanta kan komawa jam'iyyar APC.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa wasu manyan ‘yan siyasa na matsa masa lamba da ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC mai mulki.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Banquet Hall na fadar gwamnati da ke Jos a karshen mako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Mutfwang zai cigaba da zaman PDP?
Mutfwang ya ce ya yanke shawarar ci gaba da zama a PDP, yana mai jaddada cewa Allah ne kaɗai da mutanen da suka zaɓe shi za su iya yanke masa hukuncin canja jam’iyya, rahoton The Cable ya tabbatar da labarin.
“Gaskiya ne suna matsa min lamba. Amma na gaya musu cewa abubuwa biyu ne kaɗai za su iya ba ni izinin barin jam’iyyata, na farko shi ne Allah Maɗaukaki, ɗayan kuma ku ne mutanen da kuka zaɓe ni.
"Ku fa, shin kun ce na tafi wani wuri ne?”
- Gwamna Caleb Mutfwang
Sai mahalarta taron suka amsa da karfi da cewa, “A’a!”
'Yan APC ba su maraba da Mutfwang
Maganganunsa sun zo ne makonni bayan jagororin APC a Plateau sun karyata rahotannin da ke cewa yana shirin shiga jam’iyyarsu.
A wani taron masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar kwanan nan a Jos, mambobin jam’iyyar sun kaɗa kuri’a tare da ƙin amincewa da wani kudiri na neman Mutfwang ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.
Gwamna ya yi wa 'yan APC martani
Da yake mayar da martani kan haka, Mutfwang ya ce waɗanda ke adawa da shi suna yin hakan ne saboda tsoro da rashin hujja.
“Wadanda ke ki na saboda abin da ban nema ba, suna ɓata lokaci ne. Gaskiya ita ce, kusan kashi 60 zuwa 70 cikin 100 na mambobin APC a Plateau za su yi farin ciki idan na shiga jam’iyyarsu."
"Sun san ba zan koma ba, shi ya sa suke jin haushi kuma suna kokarin karkatar da maganar."
- Gwamna Caleb Mutfwang
Ya kara da cewa ba ya son yin dogon bayani a kai saboda labari ne da zai bada wata rana.

Source: Facebook
PDP tana rasa gwamnoni zuwa APC
Tun bayan zaɓen 2023, PDP ta rasa gwamnoni uku da aka zaɓa a karkashinta zuwa jam’iyyar APC.
Gwamnonin sun haɗa da Umo Eno na Akwa Ibom, Sheriff Oborevwori na Delta, da Peter Mbah na Enugu.
Haka kuma, Duoye Diri na Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP, kuma ana hasashen zai koma jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana
Kusoshin APC, PDP sun fice daga jam'iyyunsu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu manyan jiga-jigan a jam'iyyar APC da PDP a jihar Plateau, sun fice daga jam'iyyunsu.
Nde Isaac Wadak, wanda ya shafe shekaru fiye da 25 yana yiwa PDP hidima, da Chief Robert Taple na APC, sun fice daga jam'iyyunsu.
Dukkanin manyan kusoshin sun bayyana dalilan da suka sanya suka raba gari da jam'iyyunsu na siyasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

