Bayan Rantsar da Shi, Shugaban INEC Ya Yi Nadin Farko a Hukumar Zaben Najeriya
- Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya yi nadin farko bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi a makon jiya
- Farfesa Amupitan ya nada gogaggen dan jarida, Adedayo Oketola a matsayin mai magana da yawun shugaban INEC na kasa
- Tun farko, Amupitan ya bayyana cewa Allah ne ya kawo shi wannan matsayi kuma zai tafiyar da INEC bisa gaskiya da amana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya nada tsohon editan jaridar Punch, Adedayo Oketola, a matsayin Mai Magana da Yawunsa.
Hakan dai na kunshe a wata sanarwa da INEC ta fitar yau Litinin, 27 ga watan Oktoba, 2025, kuma wannan ne karo na farko da sabon shugaban hukumar ya yi nadi bayan kama aiki.

Source: Twitter
Amupitan ya yi nadin farko a INEC
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Oketola ya maye gurbin Rotimi Oyekanmi, wanda ya rike wannan mukami a lokacin tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oketola, wanda dan jarida ne mai kwarewa kuma gwarzon da ya ci kyaututtuka da dama, yana da gogewa ta shekaru 20 a harkar jarida, tattalin arziki, da shugabanci.
Kafin wannan mukami, Oketola ya kasance editan Punch, okacin da jaridar ta lashe kyautar Jaridar Shekara a taron Nigeria Media Merit Awards (NMMA) na 2023.
Shi ma kansa an karrama shi a wancan lokaci da kyautar Gwarzon Editan Shekara.
Mukamai da nasarorin Oketola
Haka kuma, ya taba rike mukamai da dama a jaridar, ciki har da Editan Labarai, Editan Kasuwanci, da kuma mataimakik editan labarai da siyasa.
A fannin kyaututtuka, Oketola ya lashe lyautar The Industry Awards’ Editor of the Year (2022), sannan kuma ya kasance sau biyu yana lashe kyautar Zimeo Excellence in Media Award a Johannesburg (2015) da Nairobi (2016).
Wannan nadi na zuwa ne bayan Shugaban INEC, Farfesa Amupitan, ya jaddada aniyarsa na gudanar da aiki bisa gaskiya, amana, da ladabi da zabe mai inganci a Najeriya.
Shugaban INEC ya sha alwashin rike amana
Da yake jawabi bayan rantsar da shi a makon da ya gabata, Farfesa Amupitan ya bayyana nadinsa a matsayin mukaddari daga Allah domin yiwa hidima ga ƙasa.
“Na zo nan ne bisa wata manufa, watakila da an ba ni zabi, ba zan karbi wannan matsayi ba. Amma daga dukkan alamu, na fahimci cewa Allah ne ke jagorantar wannan ƙasa, kuma zuwa na nan alheri ne.
"Idan Allah ya ce ka tafi, waye kai da za ka ce a’a? Na zo domin na ba da gudummuwa wajen gina sabuwar Najeriya.”
- Farfesa Amupitan.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa hadin kai, gaskiya, da gudanar da zabubbuka cikin sahihanci su ne za su kasance ginshiƙan mulkinsa a hukumar INEC, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Tinubu ya ja hankalin shugaban INEC
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bukaci sabon shugabann INEC da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya, amana da biyayya ga doka, tare da kiyaye martabar hukumar.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC mai jiran gado ya isa fadar shugaban kasa da ke Abuja, an samu bayanai
Mai girma Tinubu ya fadi haka ne a wurin rantsar da Farfesa Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC ranar Alhamis da ta gabata a fadar shugaban kasa.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tun daga shekarar 1999, Najeriya ta samu ci gaba wajen karfafa tsarin dimokuradiyya da hukumomin gudanar da zabe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

