Peter Obi Ya Ce An Yi Abin Kunya a Filin Wasan Kebbi da aka Gina da Kudin FIFA

Peter Obi Ya Ce An Yi Abin Kunya a Filin Wasan Kebbi da aka Gina da Kudin FIFA

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana takaicinsa kan yadda cin hanci da rashawa ke lalata ci gaban harkokin wasanni a Najeriya
  • Ya ce rahoton FIFA kan yadda aka wawushe kudin da aka bayar domin gina filaye da bunkasa matasa abin kunya ne ga kasa baki daya
  • Jagoran jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya zargi shugabannin da ke satar dukiyar kasa da zama asalin 'yan Yahoo masu durkusar da cigaban kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa a bangaren wasanni tamkar madubin halin da Najeriya ke ciki ne gaba ɗaya.

Ya ce satar kudin da ake bayarwa domin bunkasa harkokin matasa da wasanni ya nuna irin yadda rashin gaskiya da rashin tsari suka mamaye gwamnati da hukumomi a kasar.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Filin wasan Kebbi
Filin wasan Kebbi da Obi ya yi magana a kan shi. Hoto: FIFA
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar a X, Obi ya ce rahoton FIFA kan yadda aka sace kudin da aka bai wa hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) abin takaici ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi: Maganar gina filin wasa a Awka

Peter Obi ya bayyana cewa a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra, FIFA ta sanar da cewa za ta gina filin wasa a Awka, wanda zai kasance cikin shirin bunkasa wasanni a Najeriya.

Ya ce gwamnatin jiharsa ta bayar da fili nan da nan domin aikin, amma daga baya ba a sake jin komai game da shirin ba.

Obi ya ce saboda amincewarsu da wannan alkawari, gwamnatin Anambra ta karkata ayyukanta zuwa gina ƙananan filaye a sassan jiha domin tallafawa matasa.

“Mun gina filayen wasan Chuba Ikpeazu da Godwin Achebe,”

inji shi.

Korafin Obi kan filin wasan Kebbi

Peter Obi ya nuna takaici kan yadda aka yi asarar $25m (₦36.5bn) na bunkasa matasa saboda satar kudi da ake samu daga FIFA da CAF tun daga shekarar 2013.

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya za ta shiga cikin lamarin karin kudin gidan haya

Ya bayyana cewa sama da dala miliyan 25 aka karɓa don ci gaban wasanni amma babu abin kirki da aka gani a kasa.

Tashar TVC ta rahoto Obi ya ce:

“Wannan da ake kira filin wasa na Dala miliyan 1.2 (N1.75bn) a jihar Kebbi abin kunya ne. Tsarin ginin bai nuna kudin da aka ce an kashe ba,”

Ya ce irin wannan almundahana ce ke lalata makomar matasa da tattalin arzikin kasa, sannan shugabannin da ke aikata hakan su ne “asalin 'yan Yahoo” na Najeriya.

Jagoran LP, Peter Obi
Jagoran 'yan adawa a LP, Peter Obi a wani taro. Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

Peter Obi ya kira gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen binciken yadda aka yi amfani da kudin da FIFA ta bayar, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu.

Kwankwaso ya yi maganar haduwa da Obi

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan zaben 2027 da za a fuskanta a Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP a shirye ta ke ta hada karfi da karfe da Peter Obi da wasu 'yan adawa.

Kara karanta wannan

Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji

Sai dai ya bayyana cewa duk wata hadaka da zai yi da wasu za ta kasance ne kan yadda za a sama wa talakawa sauki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng