Sanata Nwoko Ya Tausayawa Masu Mata 1, Ya Fadi Muhimmancin Kara Aure

Sanata Nwoko Ya Tausayawa Masu Mata 1, Ya Fadi Muhimmancin Kara Aure

  • Sanata Ned Nwoko ya ce yana tausayin maza masu mace ɗaya saboda a cewarsa, auren mata fiye da haka na sa kwanciyar hankali
  • Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi kwanaki kadan bayan sabani da daya daga cikin matansa, Regina Daniels
  • Nwoko ya ce yana alfahari da matansa hudu kuma bai taɓa nadama ba kan yadda ya zaɓi tsarin aurensa na fiye da mace daya ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, AbujaSanata Ned Nwoko, wanda ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana cewa yana tausayin maza masu mace ɗaya.

Sanatan ya bayyana haka ne yana mai cewa tsarin auren mace daya ba ya samar da kwanciyar hankali ga rayuwar aure.

Kara karanta wannan

'Ka da ku biya kuɗin fansa': Gargaɗin Malami idan ƴan bindiga suka sace shi

Sanata Ned Nwoko
Sanata Ned Nwoko yana wani jawabi. Hoto: @Prince_NedNwoko
Source: Instagram

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, inda ya magantu kan zaman aure da rayuwar ma’aurata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina tausayin maza masu mata 1” — Nwoko

Sanata Ned Nwoko ya kwatanta maza masu mace ɗaya da mutum mai tsayuwa da ƙafa ɗaya a duniya.

Daily Trust ta rahoto ya ce:

“Ina tausayin waɗanda ke da mata ɗaya. Ka ɗan yi tunanin mutum mai tsayuwa da ƙafa ɗaya — hakan da wahala.
Amma idan kana da biyu, uku, ko huɗu, kana samun kwanciyar hankali. Wannan shi ne misalin da nake bayarwa.”

Lokacin da mai gabatar da shirin ya tunatar da shi cewa Bible bai amince da auren mace sama da daya ba, sai Nwoko ya ce:

“Tsohon alkawari ya amince. Ni mutum ne mai imani. Amma ba wannan ne abin da muke tattaunawa a kai ba.”

'Babu nadama kan auren mata 4,' Nwoko

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Wike ya fadi sharadin zama shaidan shugaban IPOB a kotu

Sanatan ya ce bai taɓa yin nadama kan matan aurensa ba, domin a cewarsa, dole mutum ya auri wanda yake so.

Ya kuma karyata rade-radin da ake yadawa cewa yana yin rikici da matansa a gida, yana mai cewa shi ba mutum ne mai cin zarafin mata ba.

Ya ce:

“Ni ba mutum ne mai tashin hankali ba. Ina girmama matana kuma ina ƙaunar su da yarana.”

Wannan jawabin nasa ya biyo bayan jita-jitar da ke cewa akwai rikici a tsakaninsa da ɗaya daga cikin matansa, jarumar fina-finan Nollywood, Regina Daniels.

Regina Daniels ta mallaki sabon gida

A gefe guda, jarumar fina-finan, Regina Daniels, ta wallafa sabon gidan da ta mallaka a shafinta na Facebook a ranar Lahadi, tana mai cewa ta saye gidanta domin samun kwanciyar hankali.

Ta rubuta cewa:

“A gidana ni sarauniya ce!”

Wannan ya biyo bayan makonni na rade-radin cewa akwai rashin jituwa tsakaninta da mijinta, Sanata Ned Nwoko.

Gidan Regina Daniels
Regina Daniels a gidan da ta mallaka. Hoto: Regina Daniels
Source: Facebook

An fasa auren mai Wushirya da 'Yar Guda

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar Hisabah a jihar Kano ta sanar da dakatar da auren Mai Wushirya da 'Yar Guda.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kakaba haraji kan masu jana'za, aure da suna? An ji gaskiyar lamari

Tun a farko dai wata kotu ce ta umarci hukumar ta daurawa mutanen aure bayan kama su da laifin wallafa bidiyon da bai dace ba a intanet.

Bayan umarnin kotun, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa suna da sharudan daura aure a hukumar Hisbah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng