Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko

Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko

- Biloniyan dan siyasa, Ned Nwoko, ya ce auren mace fiye da daya yana da matukar amfani domin taimakon juna ne

- A cewar dan siyasan, auren mace fiye da daya na sa a tallafi mata kuma hakan na hana su fadawa muguwar rayuwa

- Ya ce babban abun birgewa shine yadda 'yan arewa ke auren mata da yawa kuma suna haihuwar yara masu yawa

Ned Nwoko, biloniyan dan siyasa kuma mijin jarumar Nollywood Regina Daniels, ya yi bayanin dalilinsa na auren mace fiye da daya da kuma auren mata masu karancin shekaru.

A wata tattaunawa da yayi da BBC Igbo, biloniyan dan siyasan yayi bayanin abinda yasa yake auren mata masu yawa.

Kamar yadda yace, dan arewa mai rufin asiri yana da a kalla mata biyu, wanda hakan yace yana hana mata fadawa muguwar rayuwa.

Kamar yadda yace: "Dan arewa mai rufin asiri yana auren mata biyu, uku zuwa hudu. Suna taimakon al'umma saboda rashin kudi na shafar mata kuma yana kaisu ga karuwanci da sauransu.

KU KARANTA: Boko Haram da 'yan bindiga: Ministan Buhari yace an samu zaman lafiya a Najeriya

Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko
Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

"Amma kuma addinin Kirista bai amince da hakan ba, shine sai ka ga dan kudu yana da 'yan mata 10."

Ya kara da cewa yadda 'yan arewa ke aure ne yasa suka kara yawan al'umma kuma hakan yasa suke da rinjaye a kasar nan.

Nwoko yayi korafin yadda wayewa tasa maza ke auren mace daya duk da al'ada bata ce hakan ba.

Ya ce: "Ina kaunar al'adata kamar yadda take. Bana son sirka ta da komai. Al'adar Ibo tana da ban sha'awa kuma zamu cigaba da habaka ta.

"Amma idan aka duba yawanmu a Najeriya kuma muka duba aure, za mu ga cewa matar Ibo tana da 'ya'ya hudu yayin da dan arewa ke da mata hudu kowacce mata tana da yara biyar-biyar. Me kuke tsammanin zai faru nan da shekaru 10 ko ashirin?"

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce jami'an tsaro sun damke wasu 'yan Najeriya dake daukar nauyin ta'addancin Boko Haram.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Talata, 30 ga watan Maris yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin na Channels.

Legit.ng ta tattaro cewa, Shehu yace jama'a za su matukar girgiza idan suka ji bayanin binciken da ake kan makuden kudin da ake turawa kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel