Sheikh Dahiru Bauchi Ya Godewa Shugaban Aljeriya da Ya Samawa Almajiransa Alfarma

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Godewa Shugaban Aljeriya da Ya Samawa Almajiransa Alfarma

  • Fitaccen malamin addinin Muslunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ji dadin taimakon Shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune
  • Shehin malamin ya miƙa godiyarsa da Abdelmadjid Tebboune ya dauki nauyin karatun ɗalibai 140 daga ƙungiyar Tijjaniyya a Aljeriya
  • Wannan shi ne karo na biyu da Shugaban Aljeriya ya amince da irin wannan buƙata ta Sheikh Dahiru Bauchi na daukar nauyin dalibai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune.

Ya yi wannan godiya ne bisa amincewa da bayar da guraben karatu kyauta ga ɗalibai 140 daga Najeriya a jami’o’in da ke Aljeriya.

Shugaban Aljeriya ya karrama buƙatar Sheikh Dahiru Bauchi
Hoton Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wannan tallafi dai ya samu ne bayan roƙon da Sheikh Dahiru ya yi ta hannun Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya nemi a tallafa wa matasan Tijjaniyya masu neman ilimi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya yi wa masu suka martani kan nada dan uwansa sarki

Sheikh Dahiru Bauchi ya rokawa dalibai alfarma

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a cikin saƙon godiya da malamin ya rattaba hannu da kansa, ya ce wannan kyauta ta wuce bayar da damar karatu kawai.

Ya kara da cewa ta ƙarfafa alaƙar yan uwantaka tsakanin kasashen Musulmai, tare da inganta musayar ilimi da fahimta.

Shugaban Aljeriya ya ba daliban Najeriya tallafin karatu
Taswirar jihar Bauchi, mahaifar Sheikh Dahiru Bauchi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Aljeriya ta zama misali wajen girmama ilimi da mutunci."

Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da cewa:

“Ina mika godiyata ga mai girma Shugaban kasa bisa yanke shawarar buɗe ƙofofin jami’o’in Aljeriya ga ɗalibai 140 na Tijjaniyya daga Najeriya.”

Sheikh Dahiru Bauchi ya yabi Shugaban Aljeriya

Malamin ya kuma yaba da irin jagorancin Shugaban Aljeriya, yana mai cewa irin wannan shugabanci abin koyi ne ainun ga sauran ƙasashen duniya.

A kalamansa:

“Irin wannan shugabanci yana ƙara ɗaukaka matsayin Aljeriya a idon duniya, ƙasa mai daraja."

Ya kara da cewa ana iya ganin kumar da Aljeriya ke da shi ta fuskar dabbaka ilimi a kan sauran ayyuka, wadda ke ƙara inganta dangantakarta da duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kogi ya yabi hangen nesan Tinubu da ya nada 'dan jiharsa hafsan sojan kasa

Wannan dai shi ne karo na biyu da ɗaliban Najeriya ke cin moriyar irin wannan guraben karatu daga Aljeriya alfarmar Sheikh Dahiru Bauchi.

Na farko daga cikinsu suna gab da kammala karatunsu a jami’o’in ƙasar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Sheikh Dahiru Bauchi ya jaddada godiyarsa bisa wannan karrama da aka yi wa daliban ta hanyar gidauniyarsa.

'Dan Dahiru Bauchi ya magantu kan Inyass

A baya, mun wallafa cewa Sayyid Ibrahim, ɗan fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa mahaifinsa ya yi magana a kan ganin Shehunsu, Ibrahim Inyass.

Ya bayyana cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba ya goyon bayan akidar da ke cewa ana iya ganin Shehu Ibrahim Inyass a bango, bishiya ko sama kamar yadda wasu ke ikirari.

A cewarsa, wannan magana yaudara ce da wasu mutane ke amfani da ita don cutar da jama’a musamman waɗanda ba su da cikakken ilimin addinin Musulunci da darikar Tijjaniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng