An Bukaci Tinubu Ya Takawa Matawalle Birki bayan ‘Gano’ Abin da Yake Kullawa
- Kungiyar dattawan Arewa ta jam’iyyar PDP ta bukaci Bola Tinubu ya takawa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle birki kan halayensa
- Dattawan suna zargin Matawalle, da lalata jam’iyyarsu ta hanyar janyo mambobi su koma APC mai mulkin Najeriya
- PDP ta bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan Matawalle, tana cewa hakan na barazana ga dimokuraɗiyya da daidaiton siyasar ƙasar nan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Kungiyar Dattawan Arewa ta PDP ta 'bankado' wani shiri da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ke yi wa jam'iyyar.
Dattawan sun nemi Shugaba Bola Tinubu da ya ja kunnen Ministan Tsaron Ƙasa, Bello Matawalle, saboda kunna musu rikicin siyasa wanda ba zai zama alheri ba ga kasa.

Source: Facebook
Zargin da ake yi wa Bello Matawalle
Sakataren ƙasa na kungiyar, Dr. Abbas Sadauki ne ya yi wannan zargi bayan taron dattawan PDP daga kananan hukumomi huɗu na Zamfara, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta zargi Matawalle da ƙoƙarin janyo mambobin PDP su koma APC musamman a jihohin Zamfara da Kaduna ta hanyar amfani da kuɗi.
Ya ce ƙoƙarin Matawalle na rusajam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma barazana ce ga dimokuraɗiyya da gasa mai tsafta.
“A matsayinsa na minista, yana amfani da mukamai da tasirin siyasa don lalata jam’iyyar mu da jan mambobin mu zuwa APC."
- Abbas Sadauki

Source: Original
Matsalar jan yan PDP zuwa jam'iyyar APC
Sadauki ya ce irin waɗannan matakai na kawo gibi a jam’iyyun adawa tare da lalata ƙa’idar siyasa mai ma’ana da gaskiya a ƙasar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya gargadi gwamnati cewa ci gaba da jan mambobin PDP zai rage bambancin siyasa da kuma gurgunta cigaban dimokuraɗiyyar Najeriya gaba ɗaya.
Ya ce:
"Irin wannan yanayi yana kawo tsaiko ga jam'iyyun wanda yake yi musu illa da kuma yin tasiri wurin fafatawa a siyasa nagartacciya.
“Rushe jam’iyyun adawa ba alheri ba ne ga dimokuraɗiyya. Shugaba Tinubu ya kira Matawalle da gaggawa kafin ya lalata tsarin siyasa.”
Yadda PDP ke rasa 'ya'yanta zuwa APC
Rahotanni daga Zamfara sun nuna cewa sama da mambobin PDP 24,000 sun sauya sheƙa zuwa APC cikin makonni da suka gabata.
Majiyoyi suka ce daga cikinsu akwai manyan shugabannin jam'iyyar da dattawa a kanananan hukumomi shida da ke jihar.
Matawalle ya yi tayin shiga APC ga Gwamna
A baya, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya tura sako na musamman ga Gwamna Dauda Lawal kan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Matawalle ya buƙaci Gwamna Lawal da ya bar PDP zuwa APC, yana cewa jam’iyyar na da nagarta da mutane masu hangen nesa inda ya ce shi ma zai ba da tashi gudunmawa.
Ministan ya fadi hakan ne a Maradun yayin da dubban magoya bayansa suka kai masa gaisuwar Sallah da ta gabata, yana mai kira kan hadin kai domin ci gaba da gudanar da ayyukan alheri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

