Tsohon Janar Ya Fadi Abin da Zai Faru a Gidan Soja bayan Tinubu Ya Yi Sauye Sauye

Tsohon Janar Ya Fadi Abin da Zai Faru a Gidan Soja bayan Tinubu Ya Yi Sauye Sauye

  • Tsohon babban jami’in soja, Manjo Janar Anthony Atolagbe (mai ritaya), ya yi magana bayan Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a rundunar tsaro
  • Anthony Atolagbe ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa garambawul da ya yi a rundunonin tsaro inda ya ce hakan ne mafi dacewa
  • Tsohon Janar din ya ce matakin ya nuna jarumta da mutunta tsarin ci gaban aiki a soji, inda ya ce zai inganta daidaituwar runduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Bayan garambawul a rundunar tsaro ta Najeriya, masana da tsofaffin sojoji na tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.

Tsohon kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Anthony Atolagbe (mai ritaya), ya yaba wa Bola Tinubu bisa sauye-sauyen da ya yi a rundunonin tsaro.

An yabawa Tinubu kan garambawul a rundunar tsaro
Bola Tinubu da tsohon hafsan tsaro, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Yayin da yake magana a shirin Politics Today na Channels TV, Atolagbe ya ce matakin ya nuna jarumta da mutunta tsarin aikin soja.

Kara karanta wannan

Kwararren mai bincike ya gano dalilan korar manyan hafsoshin tsaron Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi gyara a rundunar tsaron Najeriya

A ranar Juma’a 24 ga watan Oktobar 2025 Tinubu ya cire Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaro, inda ya nada Janar Olufemi Oluyede a madadinsa.

Shugaban ƙasa ya kuma nada Janar Waidi Shaibu a matsayin sabon Babban Hafsan Sojoji, tare da sababbin shugabanni ga rundunar ruwa da jiragen sama.

Wannan garambawul ya jawo maganganu inda wadansu ke zargin sauye-sauyen bai rasa nasaba da zargin juyin mulki a kasar.

Sai dai gwamnatin kasar ta musanta labarin cewa an yi sauye-sauyen ne saboda fargabar juyin mulki.

Tsohon soja ya yabawa Tinubu kan korar wasu sojoji
Shugaban kasa, Bola Tinubu a birnin Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tsohon Janar ya fadi dalilin korar shugabannin tsaro

Lokacin da aka tambaye shi ko an yi wasu nade-naden ne saboda siyasa, tsohon Janar ɗin ya ce zabin shugabannin ya dogara da cancanta.

Ya bayyana cewa sababbin hafsoshin tsaron sun dace da mukamansu, domin tsarin ci gaban aiki yana tabbatar da daidaito da ci gaba cikin ayyukan tsaro.

Kara karanta wannan

Sauya manyan sojoji zai iya jawo sama da Janar 60 su yi murabus a Najeriya

Ya ce:

“Wannan babban mataki ne, domin zai taimaka wajen tabbatar da bin ka’idojin aiki da ci gaban manyan jami’an sojoji cikin tsari.
"Idan jami’ai sun daɗe a wasu mukamai, hakan yana rage damar waɗanda ke biye da su. Shugaba Tinubu ya yi abin yabawa.”

Atolagbe ya ce sababbin shugabannin sun san yanayin tsaro na ƙasar sosai, domin duk sun fito daga fagen yaƙi tare da ƙwarewa ta musamman, cewar TheCable.

Sauye-sauyen sun zo ne makonni bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki wanda rundunar soji ta ƙaryata a fili cikin sanarwarta ta baya-bayan nan.

Dalilin Tinubu na korar hafsoshin tsaro

Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da tsokaci kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na sauya kusan dukkanin hafsoshin tsaron Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa korar da Shugaba Tinubu ya yi musu, ba ta da alaka da jita-jitar yunkurin juyin mulki da ake ta yadawa a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kogi ya yabi hangen nesan Tinubu da ya nada 'dan jiharsa hafsan sojan kasa

Ta bayyana cewa Bola Tinubu yana da ikon nadawa tare da korar duk wanda ya ga dama idan ya bukaci yin hakan domin sake inganta bangaren tsaron kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.