Jami’ar Ahmadu Bello Ta Yi Magana kan Jita Jitar Kera Makamin Nukiliya a Sirrance
- Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta yi magana kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ya zarge ta da kera makamin nukiliya
- A wata sanarwa, jami’ar ta ce bidiyon na karya ne, kuma AI ne ya kirkire shi don ya yaudari jama’a game da shirin makamashin nukiliya na Najeriya
- ABU ta bayyana cewa ayyukanta na nukiliya suna karkashin kulawar IAEA kuma suna da manufar zaman lafiya, ba kera makami ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta warware jita-jitar da ake yadawa game da kera makamin nukiliya ga Najeriya.
Jami'ar ta karyata wani faifan bidiyo da ke cewa tana da hannu wajen kera makamin nukiliya a Najeriya a sirrance.

Source: Twitter
An yada bidiyon zargin ABU da kera nukiliya
Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar wanda shafin jami'ar ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bidiyon, wanda aka kirkira ta fasahar AI, ya buga bayanai na ƙarya da nufin ruɗar da jama’a game da shirin makamashin nukiliya na ƙasa.
Bidiyon ya yi zargin cewa masana kimiyya na Najeriya a shekarun 1980 sun ɓoye uranium a Kaduna tare da taimakon cibiyar ABU.
Nukiliya: Jami'ar Ahmadu Bello ta musanta jita-jitar
Umar ya ce wannan zargin ba shi da tushe ko hujja, domin yawancin masana jami’ar a lokacin suna karatu a ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa ABU ba ta taɓa samun alaƙa da hanyar AQ Khan ta Pakistan ba, kuma ba ta taɓa karɓar kayansu ba.
Umar ya ce a shekarar 1987, abin da ke ABU kawai shi ne injin '14 MeV Neutron' wanda ya fara aiki a 1988.
Ya bayyana cewa an kafa injin nukiliya na farko a Najeriya ne a 1996 ƙarƙashin shirin haɗin gwiwa da Hukumar IAEA.

Source: Twitter
Abin da Jami'ar Ahmadu Bello ta sanya a gaba
Jami’ar Ahmadu Bello ta tabbatar da cewa duk ayyukan nukiliyarta na lumana ne bisa yarjejeniyar kasa da kasa da ke haramta kera makaman nukiliya.
Umar ya ce Cibiyar Bincike da Horarwa ta Makamashi da aka kafa a 1976 tana aiki tare da IAEA da abokan hulɗa daga Amurka, Rasha da China.
Ya tabbatar da cewa jami’ar ba ta taɓa shiga shirin kera makami a boye ba, domin manufarta ita ce amfani da ilimi don ci gaban ƙasa.
Umar ya jaddada cewa jami’ar za ta ci gaba da tallafa wa kimiyya da fasaha don amfanin ɗan adam da ci gaban Najeriya cikin lumana.
Najeriya ta karyata kera makamin nukiliya
A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta ce ba ta da shirin ƙerawa ko gwajin makaman nukiliya yayin da ake fadan Isra'ila da Iran.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya faɗi matsayar Najeriya da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar CTBTO a Abuja.
Wannan dai na zuwa ne bayan zargin kasar ta na shiri a karkashin bayan barkewar yaki tsakanin Iran da Isra'ila, wanda ya samu asali daga shirin kera nukiliya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


