Tuna Baya: Namijin Kokarin da Janar Shuaibu Ya Yi kafin Zama Hafsan Sojojin Kasa

Tuna Baya: Namijin Kokarin da Janar Shuaibu Ya Yi kafin Zama Hafsan Sojojin Kasa

  • Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Waidi Shuaibu a matsayin sabon hafsun sojojin asa don ƙarfafa yaƙi da ta’addanci
  • Janar Shuaibu ya samu nasarori da dama a lokacin da yake jagorantar dakarun Operation Hadin Kai a Arewacin Najeriya
  • A wannan rahoto, Legit Hausa ta tsakuro wasu muhimman abubuwan bajinta da Shuaibu ya yi kafin zama hafsun soja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja — Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Manjo Janar Waidi Shuaibu a matsayin sabon hafsun sojojin kasa (COAS), wanda zai fara aiki daga ranar 24 ga Oktoba, 2025.

Janar Waidi Shuaibu ya gaji Janar Olufemi Oluyede, wanda aka ɗaga matsayinsa zuwa babban hafsun tsaron kasa (CDS) bayan shekaru na aiki da sadaukarwa a rundunar soja.

An zakulo abubuwan bajinta game da sabon hafsan sojojin kasa, Janar W. Shuaibu
Hoton sabon hafsun sojojin kasa, Manjo Janar Waidi Shuaibu. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

OPHK: Namijin kokarin Janar Shuaibu

Kara karanta wannan

Janar Undiandeye: Sojan da ya tsira da kujerarsa da Tinubu ya kori hafsoshin tsaro

Mai sharhi kan lamuran tsaron Arewa maso Gabas da yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya wallafa wasu bayanai game da Janar Shuaibu a shafinsa na intanet.

Rahoton ya nuna cewa, Manjo Janar Waidi Shuaibu wanda haifaffen jihar Kogi ne ya yi ayyukan bajinta kafin nada shi hafsun sojoji, da suka hada da:

1. Jagorancin Operation Hadin Kai (OPHK)

Tun lokacin da aka naɗa shi Kwamandan Operation Hadin Kai (OPHK) a Arewa maso Gabas, Manjo Janar W. Shuaibu ya nuna ƙwarewa da hangen nesa wajen yaƙar ta’addanci.

A karkashin jagorancinsa, sojoji sun kai manyan hare-hare cikin nasara a Dajin Sambisa da Tumbuktu Triangle, inda aka lalata mafakar ’yan ta’adda da katse hanyoyin samar musu da makamai.

2. Gyaran kayan aiki da karfafa runduna

Janar Shuaibu ya jagoranci gyara da sabunta manyan kayan aikin soja, ciki har da motocin yaki kirar APC guda 10, Steyr APC guda 3, da MRAP guda 6.

Wannan gyara ya taimaka wajen ƙarfafa rundunonin soji musamman kamar 199 Special Forces Battalion da 25 Brigade.

3. Murkushe ’yan ta’adda da ceto mutane

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da sababbin hafsoshin tsaron Najeriya a Aso Rock

Rahoto ya nuna cewa rundunar Janar Shuaibu yake jagoranta ta hallaka ’yan ta’adda 567, ta kwato makamai 492 da harsasai fiye da 10,000.

Haka kuma, sojoji sun ceto mutane 2,225 daga hannun ’yan ta’adda, sannan akalla 'yan ta'adda 121,000 da iyalansu suka mika wuya ga rundunarsa.

A fannin bincike da leƙen asiri, Janar Shuaibu ya yi amfani da jiragen NAF UAV da jiragen ISR 760, wajen samun bayanan da suka taimaka wajen kai hare-hare cikin nasara.

Dakarun sojojin Oeperation Hadin Kai sun samu nasarori masu yawa kan 'yan ta'adda.
Dakarun sojojin Najeriya sun kai samame a wasu yankunan da 'yan ta'adda suke buya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

4 Hadin gwiwar sojoji da jama’a

Wani abin birgewa shi ne, Janar Shuaibu ya kafa gasar karatun Alƙur’ani don ƙarfafa haɗin kai da ɗabi’un addini tsakanin dakarun soja da mutanen gari.

Ya kuma ƙaddamar da Operation Desert Sanity III daga Fabrairu zuwa Yunin 2024, wanda ya haifar da zaman lafiya a Kukawa, inda mutane 4,000 daga sansanonin ’yan gudun hijira suka koma muhallansu.

5. Kashe manyan shugabannin ta’addanci

Sojojin da Janar Shuaibu ke jagoranta sun yi nasarar kashe manyan shugabannin 'yan ta'adda, ciki har da Tahir Baga da Abu Rijal a cikin 2024, wanda hakan ya raunana ikon ’yan ta’adda sosai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An kama dalibin jami'ar IBB kan saboda gwamna a Facebook

Saboda wannan gagarumar nasara, rundunar OPHK ta Arewa maso Gabas ta lashe kyautar Security Watch Africa a Disambar 2024, a matsayin rundunar tsaro mafi inganci a Afrika.

Dalilin Tinubu na sauya hafsoshin tsaro

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da babban sauyi a tsarin shugabannin rundunonin tsaro na ƙasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumma’a, 24 ga Oktoba, 2025, Tinubu ya tabbatar da naɗin Janar Olufemi Oluyede a matsayin shugaban tsaron kasa (CDS).

Tinubu ya ce wannan sauyin “zai ƙarfafa tsarin tsaro na ƙasa” tare da tabbatar da haɗin kai da nagartar jagoranci a cikin dakarun Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com