Nnamdi Kanu: Wike Ya Fadi Sharadin Zama Shaidan Shugaban IPOB a Kotu
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana damuwa game da sanya sunansa cikin wadanda za su ba da shaida a kotu
- Wike ya ce ba zai bayyana a kotu a shari’ar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ba saboda kawai sunansa ya fito a jarida
- Ministan ya ce zai halarci kotu ne kawai idan aka ba shi sammaci a hukumance, yana mai jaddada cewa dole ne ya mutunta umarnin kotu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi fatali da maganar zuwa kotu domin ba da shaida kan shari'ar Nnamdi Kanu.
Wike ya bayyana cewa ba zai bayyana a kotu a shari’ar shugaban IPOB din da ake tuhuma ba saboda kawai sunansa ya fito a jarida ba.

Source: Getty Images
Yayin taron manema labarai a Abuja da Channels TV ta bibiya, Wike ya ce ba wanda ya ba shi takardar kiran kotu ko wata doka da ta bukaci ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da me ake tuhumar Nnamdi Kanu a kotu?
Mazi Kanu, wanda mutumin Najeriya ne da kuma ƙasar Birtaniya, yana fuskantar tuhumar ta’addanci wajen kira da yake yi na neman ’yancin kai ga yankin Kudu maso Gabas.
An fara kama shi a watan Satumban 2015 saboda shirye-shiryen rediyo da yake yi yana goyon bayan ballewar yankin Igbo daga Najeriya domin kafa ƙasar Biafra.
Daga baya an ba shi beli amma ya gudu daga ƙasar a 2017 bayan wani samame da sojoji suka kai garinsa na jihar Abia.
An sake cafke shi a 2021, kuma tun daga lokacin yana hannun hukumar DSS, daga nan shari’arsa ta shiga hannun alkalai huɗu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tare da sauye-sauyen lauyoyinsa masu kare shi.

Source: Facebook
Kanu: Abin da WIke ke jira daga kotu
Wike ya ce, zai bi umarnin kotu ne kawai idan an kira shi da sammaci na doka don bayar da shaida ko gabatar da hujja, cewar Punch.
Ya ce:
“Ba saboda na ga sunana a jarida zan fara gudu ba. Idan kotu ta bukace ni da sammaci, dole ne na halarta."
Da aka tambaye shi dalilin da yasa Nnamdi Kanu ya lissafa sunansa cikin shaidu, Nyesom Wike ya ce shi kansa bai san dalili ba.
Ya ce shi bai taba magana da shi ba cewa yana son ya ba da shaida a kotu game da abin da ake tuhumarsa a kai.
“In ka ga Nnamdi Kanu, ka tambaye shi, me yasa ka saka sunana?’ Ban taba cewa ina son zama shaida ba.”
- Nyesom Wike
Me gwamnoni za su 'fada' a shari'ar Kanu?
Mun ba ku labarin cewa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya fitar da jerin shaidu yayin da ya ke shirin kare kansa a shari’ar ta’addanci da gwamnatin Najeriya ke yi da shi.
An bayyana cewa a cikin jerin akwai tsofaffin ministoci, hafsoshin tsaro da gwamnoni da suka hada da Abubakar Malami, T.Y. Danjuma da Tukur Buratai.

Kara karanta wannan
Nnamdi kanu: An gano abin da Buratai, gwamnoni da wasu manyan kasa za su fada a kotu
Shaidun za su bayar da bayani kan yadda aka kama Kanu, yadda aka haramta IPOB, da kuma abubuwan da wasu batutuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

