'Sun Yi Laifi,' An Sallami Jami'an Hukumar Shige da Ficen Najeriya 11 daga Aiki
- Hukumar da ke kula da hukumomin tsaron cikin gida ta kori jami’an shige da fice 11, ta kuma tilasta wa wasu yin ritaya
- Jami’an 11 sun rasa mukamansu ne bayan da hukumar CDCFIB ta same su da aikata manyan laifuffuka daban daban
- CDCFIB ta kuma ladabtar da wasu jami'an NIS 21, yayin da ta ce za ta ci gaba da yin haka ba tare da nuna banbanci ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da hukumomin NSCDC, NCS, FFS da NIS (CDCFIB) ta amince da ladabtar da jami’an shige da fice 31 saboda aikata manyan laifuffuka daban-daban.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Akinsola Akinlabi, jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

Source: UGC
An sallami jami'an NIS daga aiki
Ya ce matakin ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa da al’amuran bai daya na hukumar (BDGPC) da ya gabatar a wani taro a ranar 11 ga Yuli, 2025, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An kori jami’ai takwas saboda munanan laifuffuka da karya dokokin hukumar, yayin da aka tilasta wa jami'ai biyar yin ritaya saboda rashin ladabi."
- In ji Akinsola Akinlabi.
Haka kuma, an rage mukaman jami’ai takwas zuwa mataki na kasa da wanda suke yanzu, sannan jami'ai biyar sun samu takardar gargadi saboda aikata laifuffuka daban daban.
An kama jami'an NIS masu satar makamai
Hukumar ta kuma yi nazari kan korafin da wasu jami’an NIS da aka kora a baya, inda a karshe ta tabbatar da korarsu bayan ta gano babu hujjar da za ta iya dawo da su aiki.
Sai dai an dawo da jami’i daya bayan ya daukaka kara kuma ya yi nasara, yayin da ake wanek wasu jami'ai biyu daga dukkan wani zargi.
A wani bangare, Akinlabi ya bayyana cewa an kori wasu kananan jami’ai biyu bayan an same su da laifin cin hanci, satar makamai da kuma garkuwa da mutane.
“An kammala binciken cikin gida a ranar 14 ga Afrilu da 4 ga Satumba 2025, kuma aka tabbatar da sun aikata laifin."
- Akinsola Akinlabi.

Source: Twitter
NIS ta sha alwashin kiyaye ladabin jami'ai
Akinsola Akinlabi ya kara da cewa, an dauki matakan ne bisa sahalewar ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, da kuma shugabar hukumar NIS, Kemi Nandap.
Akinsola Akinlabi ya ce:
“Za mu ci gaba da tabbatar da ladabi da bin doka a dukkan matakai na ma'aikata ba tare da son kai ko nuna bambanci ba."
A watan Yuli, shugabar NIS, Janar Nandap ta bayyana cewa ana daukar matakin ladabtarwa kan jami’an da suka bai wa ‘yan kasashen waje fasfo ɗin Najeriya.
Jami'an NSCDC, NIS sun yi garkuwa da mutum
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sandan Enugu sun kama Juliet da Ngozi Chukwu, ‘yan uwa mata daga Ebonyi, bisa zargin su sace dan uwansu.
An rahoto cewa Juliet na aiki da hukumar NSCDC, sannan Ngozi na aiki a hukumar NIS, kuma sun kitsa sace babban yayansu Friday Chukwu a Ituku-Ozalla.
'Yan sanda sun cafke matan ne a wani dakin otel yayin da suke kasafta wani kaso daga cikin Naira miliyan 30 da suka karba na kudin fansar dan uwan nasu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


